A ILMIN GADO AKWAI ABIN DA AKE KIRA: MAS’ALAR DAN’UWA MAI ALBARKA, DA MAS’ALAR DAN’UWA MASH’UMI

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

1. A cikin Ilmin gado akwai abin da Malamai ke kira “Mas’alar Dan’uwa Na jini Mai albarka”, da kuma “Mas’alar Dan’uwa Na jini Mash’umi”.

2. Misalin Mas’alar Dan’uwa Na jini Mai albarka shi ne:-
Namiji ne zai mutu sannan ya bar magada kamar haka:
– ‘Ya’yansa mata biyu wadanda ya haifa da kansa.
– Jikarsa wacce dansa na tsatso ya haifa.
– Jikansa wanda dansa na tsatso ya haifa.

A nan sai a raba dukiyar da ya bari kashi 6 sai a dauki kashi 4 cikin shidan watau thuluthi biyu nata a ba wa ‘ya’yansa mata biyun. Abin da zai rage shi ne kashi 2 cikin shida na dukiyar, to sai a dauke su a ba wa diyar dansan, da kuma dan dansan. Su kuma sai su raba su zuwa kashi 3 macen ta dauki kashi 1 shi kuma namijin ya dauki kashi 2.

Da ba don wannan dan’uwa nata namijin ba to da ba ta sami kome ba; saboda gwaggwaninta tuni sun riga sun dauki thuluthi biyun da da ma shi ne kaso mafi yawa da mata ke iya samu a matsayin faradhi watau rabo.
Saboda wannan alheri da wannan dan’uwa nata ya kawo mata na samun gado shi ya sa Malaman gado suke kiran shi da sunan “Dan’uwa Mai Albarka”.

3. Misalin Mas’alar Dan’uwa Na jini Mash’umi shi ne:-
Mace ce za ta mutu ta bar magada kamar haka:
– Mijinta.
– Yar’uwarta shakikiya watau wacce suke uwa daya uba daya.
– Dan’uwanta Li’abi watau wanda suke uba daya kawai da ita.
– ‘Yar’uwarta Li’abiya watau wacce suke uba daya kawai da ita.

A nan sai a raba dukiyar da ta bari kashi 2, a ba wa mijinta kashi 1, a kuma ba wa shakikiyarta watau wacce suke uwa daya uba daya da ita kashi 1 da ya rage, ita kuma li’abiyarta, da li’abinta ba su da kome cikin dukiyar.

To amma da babu li’abi namijin sai li’abiya macen to da ita li’abiya macen ta samu kason abin da ake kira cikon thuluthi biyu ta hanyar “Aulu”, watau da sai a raba dukiyar kashi 7, a ba wa miji kashi 3, a ba wa shakikiya kashi 3, sannan a ba wa ita li’abiyar kashi 1 da ya rage.

Ke nan wannan dan’uwa li’abin mamaciya ya zan sanadiyyar hana ‘yar’uwarsa li’abiyar mamaciya samun kome daga cikin gadon; saboda wannan dalilin ne Malaman ilimin gado suka sa masa suna: “Dan’uwa Mash’umi”.

Allah Ya taimake mu har kullum. Ameen.

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started