
Kamar yadda wani mawaki yayi wata waka mai suna “Ta Leko Ta Labe” haka suna dalibai masu daukar jarrabawar NECO a Jihar Kano Ta Leko Ta Labe.
Gwamnatin Ganduje ta bakin kwamishinan yada labarai ya shelantawa jama’a biyawa dalibai fiye da dubu 38 Kudin jarrabawar NECO amma yau an wayi gari kwamishinar ilimi tace sai masu credit 5 ciki harda turanci da lissafi.
Wannan ya jawo kace-nace a fadin Jihar Kano, inda masu adawa da Gwamnatin suka fara tumurmusarta.
