Rikicin Cacar Baka Ta Barke A Fadar Mundubawa

Bayan fitar da wata sanarwa daga wani shafin sada zumunta na facebook da twitter masu lakani da tsohon malamin gwamnan kuma sabon Sanatan Kano ta tsakiya wato Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano.

Wannan sanarwa ta danganta Malam Ibrahim Shekarau da goyawa daya daga cikin masu neman kakakin majalisar dattawa Ahmad Ibrahim Lawan baya, itace ta tada kura tare da baiwa LABBA iska.

Wani tsagin masu baiwa LABBAN iska basu gamsu da sahihancin waccan sanarwa ba, harma suna cewa ba da yawun Mallam Ibrahim Shekarau din aka yi ta ba, a inda daya bangaren ke ikirarin sanarwa sahihiyace kuma da yawun Sardaunan aka yi ta.

Ya zama wajibi magoya baya su fahimci siyasa tare da biyayya ga shugabanninsu, haka kuma Shugaban Mundubawa Sanata Mallam Ibrahim Shekarau, ya fitar da wata kafar sadarwa ta masamman wacce zata bayyana sahihin labarai daga bakinsa domin gudun fadawa rudanin cikin gida da magoya baya zasu iya afkawa.

#Qalubale

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started