Yayin da wani mai ganganci ya aikata gangancinsa akanka ko akan wani dan’uwanka ko akan dukiyarka, a guje masu kallon abinda ya faru zasu taso suna baka hakuri.
Yayin da aka baka hakuri ma’ana an cutar dakai, kodai cikin ganganci ko cikin rashin sani, amma cikin masu baka hakurin babu wanda zai nunawa wanda ya aikata wannan gangancin laifisa, ballantana kai da aka yiwa gangancin kaji dadin yin hakurin da akeso kayi.
Idan kace baka hakuri ba, sai kuma reshe ya juye da mujiya, sai kuma kazama kaine mai laifi a wajen masu baka hakurin saboda an baka hakuri baka hakura ba.
Wannan shine daya daga cikin Qalubale da muke fuskanta.
