
Yan sanda sunce sun kama makamai da suka hada da takubba, wukake, adduna da kuma kwayoyin da ake sha domin buguwa a ofisoshin jam’iyyun PDP da APC yayin da suka kai wani sumame a Karamar Hukumar Tudunwada a Jihar Kano.
Hukumar Yan sandan ta Jihar Kano ta bakin kakakinta DSP Haruna Abdullahi sunce, sun kai sumamen domin kokarin karkade miyagun ayyuka, haka kuma sun damke yan bangar siyasa guda hudu-hudu wadanda ake tuhuma da mallakar wadannan makamai a kowace sakatariya ta jam’iyoyin na PDP da APC.
A gefe guda Shugaban Jam’iyyar APC da Sakatare na riko a Jam’iyyar PDP sun karyata labarin cewa, ba mutanen su bane, kuma dama an saba yi musu wannan kazafi domin a kamasu ba tare da aikata laifin komaiba tun bayan kammala zabe bi-da-bi
