Soyayyar Al’ummar mu Itace Kangaba

Wani labari da muka samu yanzu ya ruwaito cewa, akwai wani Bature mazaunin Najeriya tsayin shekaru 22 wanda yayi niyyar komawa garinsu a Kasar Turai.

Wannan Bature yana da maigadi ‘dan Najeriya wanda suka shafe tsayin wadannan shekaru tare, yana masa aikin gadi, sai Bature ya kira maigadi yace, nifa zan koma kasarmu don haka ka nuna inda kakeso zan gina maka gidan zama kai da iyalinka.

Abin mamaki sai maigadi yace shidai yafi bukatar Bature ya taimakawa Al’ummar garinsu ya samar musu da ruwan sha shine abinda yake ci musu tuwo a kwarya maimakon ya gina masa gida shi da iyalinsa kadai.

Nan take Bature ya amince, sukaje garin su maigadi aka nemi wajen da ya dace aka samar musu da yadda zasu sami ruwan sha, jin dadin da Bature yayi na ganin yadda maigadi ya damu da Al’ummar sa, sai yace da maigadi duk da samar musu da ruwan sha din da yayi ya kuma mallaka masa wannan gidan da shi Bature yake yake ciki.

Qalubale:

Mai gadi ya sami abubuwa guda biyu maimakon guda daya.

Mai gadi ya nuna soyayyar Al’ummar sa maimakon soyayyar kansa.

Bature ya nunawa mai gadi sadaukar da son rai zai iya samarwa mutum bukatarsa ta rayuwa.

Shin haka Al’ummar mu sukeyi a halin yanzu?

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started