Neman Qahon Kare

A wata makaranta ne awaki 3 suka shigo domin yin kiwo, sai wasu ‘yan makarantar suka gansu, suka kamasu sai suka yanke shawara su yi wa awakin shaida.

Suka nemi fenti suka zanawa kowacce daya daga cikin awakin lamba a jikinta kamar haka; ta fari aka zana mata lamba (1) ta biyu lamba (2) sai ta uku lamba (4) bayan sun zanawa kowacce lambar ta sai suka sakesu, kowa ya tafi abinshi.

Awaki suka tafi cikin makarantar sukaci gaba da kiwonsu, bayan tsayin wani lokaci, sai mahukuntar makarantar suka shigo domin duba dalibai da sauransu, suna zagawa cikin makarantar sai sukayi karo da awakin.

Mahukuntan sukayi mamaki yadda awaki suka shigo makarantar, sai suka bada umarnin a kama awakin a fiddasu daga makarantar, nan take ma’aikata suka kamasu, amma abin mamaki shine kowacce akuya akwai lambarta a jikinta.

Ga mai lamba 1, ga mai lamba 2, ga mai lamba 4, amma babu mai lamba 3, shine akace to mai lamba 3 tana cikin makarantar lallai a nemota, akayi neman duniya ba’aga mai lamba 3 ba, haka akayi ta nema har tsayin dogon lokaci, harma takai kara fito da sauran ma’aikatan makarantar domin tsaurara bincike amma shiru ba’a sami mai lamba 3 ba, dalili kuwa saboda dama can babu ita.

Wannan Qalubale ne ga Al’ummah a harkar rayuwa, ilimi, kasuwanci, aikin yi da sauran abubuwa.

Ya zama wajibi mu tsaya akan abinda yazo hannunmu, mu daina hangen abinda bamudashi domin samun nutsuwa da zaman lafiya da cigaba a rayuwarmu.

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started