Meyasa Ake Dora Babba Akan Karami?

NIJERIYA KASAR MAHUKUNTA

A duk lokacin dakaga Hukumomi a Nijeriya sun bawa abu Muhimmanci zakaga sune wadanda zasufi cin moriyar wannan lamarin, kai kace tattalin arzikin Nijeriya an samarda shi ne don masu madafun iko.

Jiya nake jin Majalisar dokokin Kano ta shigar da Kudurin samarwa Speaker da Mataimakin sa tabbataccen Fansho na Mutu ka raba.

Magana ta gaskiya akwai rashin dacewa cikin wannan yunkuri, kowa yasan duk wani Dan Majalisa zama yake tamkar Attajiri idan yana kan mulki da bayan saukar sa, musamman idan yayi hawa sama da daya.

Da ace Talakawa suna da Muhimmanci a wurin ‘Yan Majalisu da dokar dawowa da Ma’aikata kudin Gero da na Rago zamuji ‘Yan Majalisar nan sun dawo da ita, Musamman ma dayake yanzu Muna cikin Ramadhan.

Sau tari zaka samu Ma’aikacin dayayi shekaru 35 na aiki yayi ritaya amma bai Mallaki gidan kansa ba, shin akwai Dan Majalisar dayake kammala zangon farko 4yrs batare da ya Mallaki gida ba balle kuma wanda yakai matsayin Speaker?

Yakamata Mahukuntan mu su farka daga irin wannan Maye na son zuciya dake bugar dasu.

Arzikin Nijeriya na kowa da kowa ne, yadda Mahukunta ke takaice shi a kansu kansu zalunci ne.

Daga Umar Faruq Muhammad

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started