ABIN KUNYAR DA KE ADDABAR AKASARIN HAUSAWAN AREWA

Daga Sayyada Muhammad Jidda

Sai ka je gun taro ka ji an kamo sunan wani ƙasurgumin tsohon ma’aikacin gwamnati ko ɗan Siyasa, ana karantowa tarihin rayuwarsa da irin gwagwarmayar da ya yi a fagen aiki da mabambantan muƙaman da ya taɓa rikewa a rayuwarsa.

Ka ji an ce tsohon kaza tsohon kaza tsohon kaza da kaza, tun daga matakin ƙasa, sai an kai ga ambato irin muƙami ko matsayi na ƙololuwa da ya taɓa rikewa a rayuwarsa, amma fa idan ka bincika da ƙyar da jiɓin goshi ka iya samun aƙalla mutum goma ko ƙasa da haka da ya iya taimakawa su ka samu aikin gwamnati ko jarin kasuwa ko tallafin yin karatu ko ƙaro karatun.

In ko ka yi sa’a ka samu ƴan mutanen da ya taɓa taimakawa sai ka ga ƙila duk daga ƴan uwansa sai dangin matarsa. Wai hakan ma shi ne me ɗan imani da ƙaunar al’ummar.

Kuma fa ƙila gogan a lokacin da ake karantowa tarihin rayuwar tasa fankama ya ke ya na yake haƙora ya na baza babbar riga wai shi nan daɗi ya ke ji ana kambama shi a cikin taron al’umma.

Kuma wani ƙarin abin haushi, su ma taron al’ummar dan rashin sanin kai, ƙila a lokacin da ake kambama shin yaƙe haƙwara su ke su na yi masa tafi raf! Raf! Raf!!! Wai ga mutum mai daraja. Kaico!

Mutum ba zai fahimci kuskurensa ba, sai ya gama riƙe muƙaman ya saki ko sun sake shi, kuma ba fata ake ba in Allah ya jarabce shi da wata jartabawa ta rayuwa sai ya rasa masu taimaka masa. Saboda shi ma babu wanda ya taimakawa.

Ba ma wannan ba, aje ma babu jarrabawar, ko irin ƴar ziyarar nan da gaisuwar nan jifa jifa da mutanen da aka taimaka su ke zuwa yi wa wanda ya taimake su bayan ya gama aiki ya dawo gida, sai ya rasa masu zuwa masa. Saboda bai yi wa kowa komai ba.

Wallahi yadda mu ke da mutane masu manya da matsakaita da ƙananan muƙamai cikin aikin gwamnati da Siyasa da kasuwanci a ciki da wajen ƙasar nan da ace za mu yi tsari me kau na tallafawa al’ummarmu, ba shakka za a samu cigaba da sauƙin rayuwa fiye da yadda ake tsammani.

Amma ɗabi’ar nan ta kƴashi da hassada da muguntar kai-da-kai ita ta ke cigaba da daƙile cigaban al’ummar Hausawa.

Allah ya kyauta ya kuma ganar da mu, ya ba mu ikon gyarawa.

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started