KA TABA YIN ZINA?

Daga Nasiru Abubakar Gombawa:

Fitinar Sha’awa kashi na 04.
Tsaya kuji irin mummunan Bala’in da zina ke haifarwa. Zina tana cikin manyan laifuffuka, wanda dukkan shariun da Allah ta’ala ya saukar sun hadu akan haramcin zina.
Al kur’ani mai girma da Sunnar Annabi (S.A.W) da dukkan Malamai sun hadu akan haramcin zina.
Qofofin zina guda biyar ne kamar haka:
1- Kallo zuwaga Abinda Allah ya Haramta.
2- Shigar batsa
3- Kalaman Batsa
4- Kebancewa da matar daba muharrama ba
5- Sha’awa Mai karfi babu aure
Allah taala yace:
“kada ku kusanci zina”
Manzon Allah (S.A.W) yace: Mai zina ba zaiyi zina ba, yayin da yake zina, sai an cire masa imani.
Abdulllah Dan Mas’ud Ra yace: Duk Al’ummar da take zina, ta jawo wa kanta fushin Allah, da halaka.
Musulunci yayi umarni da tsare abubuwa guda shida sune kamar haka:
1-Addini.
2-Dukiya
3-Rayuka
4-Hankali
5-Mutunci
6-Nasaba
Amma zina ita kadai, tana rusa wadannan duka. Hukuncin mazinaci, mai aure kisa ta hanyar jifa. Saurayi mara aure Bulala dari da daurin shekara.
Ana tabbatar da zina ta hanya uku.
1-Shaidu guda hudu.
2-Mutun yayi ikirari da kansa.
3-Samun mace da ciki, babu aure, ko shubha.
Bisa sharudda da aka sanyawa ko wanne. Zina wata babbar musiface da bala’i da dukkan sharri, datake ruguza al’umma, take wargaza iyali, take tarwatsa gari, take rushe mutunci, take jawo karayar tattalin arziki, da fatara, da tsiya, da annoba, acikin rayuwar dai dai ku, da gidaje, da unguwanni, da gururuwa, da kasashe, da duniya baki daya.
Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake samun dukkan sharri kamar haka:
1- Raunin Addini
2- Raunin Akida
3- Karancin Imani
4- Rashin kunya
5- Rashin kishi
6- Rashin mutunci
7- Rashin kwarjini
8- Rashin hasken fuska
9- Duhun zuciya
10- Rashin kima
11- Rashin Nagarta
12- Rashin Nutsuwa
13- Rashin Amana
14- Fushin Allah
15- Cikawa babu imani
16- Azabar Allah.
Allah ya tsare mu da zuriyar mu, da dukkan
al’ummar musulmi daga afkawa bala’in zina.
Wadanda sukeyi Allah ya shiryesu.
Gabatarwa:-
Assalafy
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
* HUDUBAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WANDA YAYI A KHUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH, SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARFA KENAN).*
*ANNABI (SAW)YA FARA DACEWA:*
“`“Ya ku mutane ku bani hankalinku, domin mai Yiwuwa bazan sake kasancewa da ku bayan wannan shekaran ba, saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda basa wannan wuri a yau.
Ya ku mutane kamar yadda kuka riki wannan wata, (na hajji) da wannan rana (ta arfa) da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa, to, haka kuma ku riki Ran Musulmi da kuma Dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa, ku maida wa Mutane kayan da suka baku Amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu su cuce ku, ku tuna fa, hakika ALLAH zai yi sakayya akan ayukakanku, ALLAH (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi.
Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye Addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka ku guji binshi akan kanana.
Ya ku jamaa hakika kuna da hakki bisa matayenku, amma suma suna da hakki bisa kanku, to hakkin su ne akanku da kuciyar dasu, Kuma ku tufatar dasu akan jin kai. ku bi dasu kyakkyawan biyarwa, ku kuma tausasa musu domin su majibintan al amurran kune, kuma mataimakan ku, Hakki ne akansu da kar su yi abota da duk wanda ba kwa so, kuma su nisanci zina.
Ya ku jama’a kuyi kyakkyawan bauta ga ALLAH (SWT) ku tsaida salloli biyar(5) na farilla, Ku Azumci Watan Ramadan ku Kuma bada zakka. Ku aikata aikin hajji in har kun sami daman yi. KU SANI FA, ko wane musulmi dan uwan musulmi ne. Dukkan ku dai dai kuke. Ba wanda yake da fifiko saman wani sai ta tsoron ALLAH, da aikata kyawawan ayyukka.
Ku tuna fa(ya ku jama’a) wata rana za ku tsaya gaban ubangijinku, domin sakamakon ayyukanku, saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da hanya madaidaiciya bayan na kau.
Ya ku jama’a ba wani annabi ko manzo da zai zo bayana kuma babu wani addini da zai zo (bayan addinin musulunci), saboda haka kuyi tunani sosai akan wannan magana dana gaya maku, kuma ku fahimce ta (sosai).
Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); ga (alkur ani) ga kuma (sunnah) ta. In kun bi wannan ba za ku ta ba bata ba. Duk Wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, suma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji magana daga karshe sufi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada.
YA ALLAH ka zamo shaida agareni, cewa na isar da aikenka zuwa ga bayinka.” Yan uwa ku watsa wannan KHUDUBAR ga yan uwa musulmi wanda kamar yau akayi ta!!!
Allah duk wanda ya tura wannan khuduba ya Allah ka sadashi da annabin MuhammadMuhammad (saw) ya Allah kabiya masa dukkan bukatunsa na alkhairi“`

#Qalubale

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started