Daga Muhammad Bello Sharada:

‘YAN sandan Najeriya sun dauki tsawon lokaci da dade wa suna kokarin cafke Alhaji Hamisu Wadume. Bincikensu ya tabbatar hamshakin dan garkuwa da mutane ne, ya yi kaurin suna a Jihar Taraba. Kwanan nan ma Alhaji Hamisu ya karbi kudin fansa naira miliyan 100 da suka karba a hannun wani da suka yi garkuwa da shi.
A sakamakon haka, aka yi shiri na musamman aka tashi tawagar Intelligence Response Team IRT wacce sufeto janar na ‘yan sanda ya kafa. Wannan sumamen an yi shi a karkashin ASP Felix Alodije.
Cikin nasara ‘yan sanda suka kamo Alhaji Hamisu Bala Wadume suka saka masa ankwa suka taho da shi. A lokacin da zasu gudanar da wannan aikin sun hada da karin ‘yan sanda a hedikwatar ‘yan sanda da ke Jalingo.
Tsautsayi, akan hanyarsu daga Ibbi zuwa Jalingo suka hadu da sojoji.
A bayanin da rundunar sojoji ta yi, ta ce waya aka yi wa su sojoji cewa ga wasu masu garkuwa sun sace Alhaji Hamisu Bala Wadume. Kuma mutanen da suka yi satar suna cikin mota Hiace mai lamba LAG MUS 564. Sojojin runduna ta 93 da ke Takum a wurin chekin guda uku sun nemi wadannan mutanen su tsaya suka ki, dole suka bi su da gudu bayan sun bude musu wuta suka rika dauki ba dadi da su. Daga karshe a sanadiyyar haka suka kashe ‘yan sanda uku da civilian daya kuma mutum hudu sun ji munanan raunuka.
Sai bayan da aka yi wannan ba- ta – kashin ne, sojoji suka gano ai ‘yan sanda ne suka zo yin aiki cikin sirri, wanda basu da masaniya akansa, kuma sun yi tambaya babu bayani, hakan har ya kai ga mutuwar wasu kwararrun aikin yan sanda da suke tare da IRT.
Amma kuma jami’an ‘yan sanda, sun ce sojoji fa karya suka tsara don haka suna da tambayoyi guda shida ga sojoji. Suna son a fada musu wanene ya yi wa sojoji waya? Suna son su sani ta yaya aka yi Alhaji Hamisu Bala Wadume ya samu kubuta? Yanzu Alhaji Hamisu Bala Wadume yana ina? Da sojoji suka kama Alhaji Hamisu Bala Wadume sun tsere shi kuma sun dauki bayaninsa kamar yadda tsarin aiki ya tanada? Yaya aka yi soja suka rika harbin ‘yan sanda alhali gasu a gabansu kuma wasu cikin yan sandan sun gaya musu aiki suka zo?
Abin takaici wadannan ‘yan sanda da aka kashe suna cikin tawagar shahararren dan sandan nan Abba Kyari da suka samu horo na kwarewa akan harkar garkuwa da ta’addanci daga kasashen duniya. Suna cikin wanda suka kamo Evans kuma kwanan nan suka tserar da Magajin Garin Daura.
An kafa kwamitin bincike akan wannan musiba a karkashin DIG Mike Ogbizi. Zamu kasa kunne mu ji, don wannan batun bai kamata ya tafi haka a banza ba. An kashe ma’aikata na musamman, sojoji su ci gaba da harkarsu shike nan, shi kuma Alhaji Hamisu Bala Wadume ya ci banza kenan, kuma zaman lafiyar da ake son samu shima babu?
Duk wadannan bayanan na samo sune a hannun Cif Frank Mba na rundunar ‘yan sanda da Hafsan soja Sagir Musa.
