
Hukumar bada hasken lantarki a Najeriya wacce duk wani dan Najeriya ke tunanin samun gamsashshan hasken lantarki daga gareta domin gudanar da harkokin yau da kullun sun gaza.
A Najeriya yanzu haka muna shafe awanni 21 daga cikin awanni 24 babu hasken lantarki, ma’ana muna iya samun hasken lantarkin ne na awanni 3 kacal a kowace rana, kai wata ranar ma gaba daya haka zamu kwana mu wuni batare da ganin hasken lantarki ba.
Wannan hukumar bada hasken lantarki tayi sanadiyar durkushewar tattalin arziki da masana’antu kanana da manya da asarar rayuka sakamakon cututtuka barkatai, sanadiyar rashin hasken lantarki.
Dukkanin hanyoyin da Gwamnati yakamata tabi domin dawo da darajar samar da hasken lantarki yakamata tabi, babu wata kasa a duniya da aka sami cigaba a cikin duhun dukununu, kananan kasashen Afirika tuni suka wuce sa’anninsu harma da yayyansu a harkar baiwa al’ummarsu hasken lantarki, wasu ma har yayi musu yawa bazasu iya shanye abinda suka mallaka na hasken lantarkin ba.

Wadanda Gwamnati ta mallakawa alhakin samar da hasken lantarkin ga al’umma sun gaza, aikin su kawai sayarwa da mutane “duhu” maimakon “haske” duk watan duniya zakaga suna zagayawa da takardun biyan kudi, inda duk wata sai kudin ya hau fiye da na watan baya.
Yaya za’ayi a gidajen talakawa masu amfani da kwan lantarki uku ko hudu a kowace rana, amma karshen wata a kawo musu takardar biyan kudi Naira dubu goma ko fiye da haka?
Muna kira ga Gwamnati suyi gaggawar chanja wata hukumar wacce zata iya gudanar da wannan aiki, Gwamnatin tayiwa al’umma alkawarin kawo chanji da cigaban rayuwarsu shine dalilin zaben da suka fito suka gudanar, ba zabe sukayi domin zama cikin duhun dukununu ba.
Qalubale@gmail.com
