AIKIN GWAMNATI DA ALBASHIN MA’AIKATA A NAJERIYA

Matasa, bayan sun kammala karatu basu da wani buri sai samun dacewa da aikin gwamnati a matsayin sakamako karatun nasu.

Shi aikin gwamnati idan muka duba, ana shafe shekaru 35 ana yinsa matukar babu wata matsala, sai dai kuma idan ya yi shekaru 60 da haihuwa, anan shima dole ma’aikacin ya ajiye aikin nasa.

Idan muka duba, shi ma’aikacin gwamnati yana shafe dukan rayuwarsa a bakin aiki, domin kuwa idan muka lissafa lokacin da ma’aikacin ya fara aiki misali yana shekaru 25 kuma ya kammala aikin bayan shekaru 35, idan mun hada shekarunsa na haihuwa zai kama 60 kenan daidai.

Shekaru 60 a duniya ba karamin abu bane, domin a lokacin babu abinda mutum ke nema a duniya sai hutu sai salatin Annabi da hailala da istigfari, ma’ana shekaru sun shude an tafi gangara sai neman daidaitawa tsakaninsa da ubangijinsa, a wannan lokaci kuma zaka dinga neman yadda zaka sami kulawar gwamnati domin ta biyaka hakkin da ya rage naka a hannunta, bayan duk kagama salwantar da rayuwar ka wajen bautawa jama’a.

Wasu mutane basu dauki aikin gwamnati aikin bautawa jama’a bane, sai lokacin da ma’aikata suka shiga takun saka da gwamnati wajen neman gwamnatin ta kara musu albashi ko alawus na aiki, anan jama’a suke gane amfanin ma’aikata a garesu, idan sunje asibiti ba likita ko a makarantu ba malamai ko abin Allah ya kiyaye ana gobara, babu ma’aikatan kashe gobara ko a gidan ruwa babu masu bude ruwan sha, dadai sauransu.

Shi kuma albashin na ma’aikata, bai taka kara ya karya ba, dayawa daga jama’a idan kace suzo ga aikin gwamnati kuma ga albashin da za’a biyasu bayan kowane wata, ba zasuyi ba, saboda albashin babu abinda zai yi musu wajen gudanar da kansu da iyalinsu, wannan albashin shine fa gwamnatocin Najeriya suke kyashin biyan ma’aikatan.

Babu wani ma’aikaci da yake jin dadin albashinsa a Najeriya saidai kawai idan yana wani bangare da kudin gwamnati ke wucewa ta gabansa, kuma baya iya kauda kansa sai ya taba, yin haka kuma haramun ne, idan ya mutu Allah zai tambayeshi, haka kuma a duniya, zai hadu da danasani yayin da yabar aiki, saboda samun irin wadannan haramtattun kudade ya kare, gashi kuma ya saba da rayuwar kece raini shi da iyalansa, shikenan kuma an shiga wani hali.

Don haka, idan muka duba, duba irin na hankali, zamu gane cewa babu wani dadi a aikin gwamnati tun daga farkonsa har karshensa sai asarar rayuwa da kayi kana aiki ba tare da ka amfani irin basirar da Allah ya hore maka ba, ta hanyar bujuro da wasu sana’oi wadanda zasu amfaneka tare da iyalinka da kuma sauran al’ummah, yakamata matasa suyi karatun tanutsu, su gane cewa aikin gwamnati shine abu na karshe da zasuyi bayan duk wata dama ta gushe daga garesu.

Kada matashi yana da kuruciya ga kaifin basira ga karfin jiki, ya batawa kansa lokaci wajen neman aikin gwamnati, saboda gwamnati zatayi ta yaudararsa wajen samar masa da albashin da zai iya taimakon kansa da iyalinsa ba tare da sun cika alkawarinsu ba, haka kuma bayan ya gama aiki ta hanashi hakkokinsa da zai amfana dasu koda wajen yin wata karamar sana’a ne, daga karshe haka zai hakura a bisa dole har wani lokaci ma ta Allah ta kasance, babu wanda zai kalli iyalinsa da yabari a raye.

Wannan shine qalubalen rayuwar aikin gwamnati da albashin ma’aikata a Najeriya.

Na’Allah Raheemeeb

Qalubale@gmail.com

7/9/2019

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started