MAGOYA BAYAN KWANKWASO SUNYI YUNKURIN HALLAKA MINISTA A NIGERIA

Daga Fa’izu Alfindiki

Abinda wasu ‘yan daba daga cikin darikar Kwankwasiyyah suka yiwa Ministan Sadarwa a Nigeria Dr Isah Ali Ibrahim Pantami jiya a filin jirgin sama na Kano yunkurin kisa ne, imba don Allah Ya kaddara jami’an tsaron da ke rakiyarsa sunyi bajinta ba wajen bashi kariya watakila da yanzu wani labarin ake na dabam.

Za’a iya tuna watannin baya lokacin da wasu ‘yan daba daga cikin magoya bayan darikar Kwankwaso suka tabbatar wa duniya cewa zasu hallaka Malam Isah Ali Pantami tun kafin ya zama Ministan Sadarwa lokacin yana matsayin Darakta Janar a ma’aikatar NITDA a tsakiyar Azumin watan Ramadan da ya gabata, sai gashi a jiya sun tabbatar mana da yunkurin kashe shi din.

Sannan sunyi kokarin su keta masa mutunci ta hanyar cire masa hula da kayan jikinsa su masa tsirara bayan jifar da suka masa da ihu da tsinuwa sai Allah Ya kubutar dashi.

Muna cike da tsoro idan basu saka wa Maigirma Minista guba (poison) ba saboda sun samu sa’ar taba jikinsa, akwai killer poison ko killer cancer disease wanda ‘yan leken asiri (spy) suke amfani dashi su saka a jikin mutumin da suke so su hallaka cikin kankanin lokaci ba tare da an gane su ba, don haka ko da wasa mu ba mu yarda da mamayar da ‘yan dabar Kwankwasiyya suka yiwa Ministan Sadarawa ba, dole ayi bincike.

A cikin birnin Kano wannan mummunan al’amari ya faru, don haka muna kira ga gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta da dauki matakin gaggawa wajen zakulo mutanen da suka jagorancin yunkurin hallaka babban mutum a tsarin dokokin gwamnatin Nigeria Maigirma Ministan Sadarwa don su fuskanci hukunci ko da sun kasancewa daga cikin wadanda aka tura Indiya ne a dawo da su gida a hukuntasu.

Sannan muna kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar daukar matakin gaggawa akan darikar Kwankwasiyya, don kiyaye faruwar abu makamancin wanda suka yiwa Maigirma Ministan sadarwa, babu shakka da sun samu sa’a hallakashi zasu yi.

Muna rokon Allah Ya cigaba da tsare mana rayuwar Dr Isah Ali Ibrahim Pantami daga dukkan sharri Amin.

Qalubale@gmail.com

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started