Daga Datti Assalafiy:

Duk wanda Allah Ya hore masa arziki da lafiyar da zai iya auren mata hudu ya rayu da su amma baiyi hakan ba saboda kwaikwayon tsarin mutanen banza ‘yan boko aqeedah, to gaskiya bai taimaki kansa ba, kuma bai taimaki al’ummah ba
Jama’a idan kuka duba halin da muke ciki yanzu, a kowani lokaci mata ninka maza suke a yawa, idan akace maza su rayu da mace daya sauran matan kuma su auri kansu kenan?
‘Yan boko aqeedah idan za’a biye ta tasu auren ma ba za’ayi ba, sai dai Zina da Luwadi da Madigo, don su a gurinsu wayewa ne, ba zaka taba rasa ‘yan boko aqeedah da dabi’ar Zina da Luwadi ba, sai kalilan daga cikin wadanda ba su rika a kidar ba
Yanzu munkai matsayin da ba’a iya banbance tsakanin ‘yan mata da zawara su wa sukafi yawa? idan za’a auri ‘yan mata kadai a kyale zawarawa, mazan zasu kare, zawarawa ba su samu masu auren su ba
Yau inda ace masu hali zasu dinga auren mata hudu to da sun taimaki al’ummah ta fuskoki da dama, zai rage sabon Allah, lalata da fasadi, zai rage yawan ‘yan mata da zawarawa da suke gaban iyayensu babu mijin aure, sun zama tamkar kishiyoyi a gurin wadanda suka tsuguna suka haifesu, kullun fada, uwa tana jinin al’ada ‘yar ta tanayi, kunga abu ai baiyi tsari ba
Don Allah jama’a masu karfin hali da lafiya ku fara tunanin taimakon al’ummah ta hanyar auren mata hudu, ga nan ‘yan mata birjik suna jiran mijin aure, sun rika har sun rike a gaban iyayensu
Ina rokon Allah Ya mana albarka, Ya bamu ikon auren mata hudu da abinda zamu iya rikesu da shi Amin
Qalubale@gmail.com
