Zamfara: Hannun Sarakuna, Sojoji da ‘yan Sanda a tada kayar baya

Ana zargin sarakunan gargajiya 5 da masarautunsu na gundumomi 33 a Jihar Zamfara wajen hada baki da ‘yan tada kayar baya, kamar yadda majiyarmu ta tsegunta mana cewa, kwamatin da gwamna ya kafa domin nemo bakin zaren, karkashin wani tsohon shugaban ‘yan sandan Najeriya Alh. M.D Abubakar.

Kwamatin M.D Abubakar ya bada shawara a sauke sarakuna 5 da dagatai 33 da masu unguwanni, haka kuma yabada shawarar a tuhumi daya daga cikin sarakunan a kotu, sannan yayi kira ga gwamnatin tarayya ta kafa kotu ta masamman domin hukunta wasu sojoji 10 da aka samu da hannu dumu-dumu cikin wannan badakala.

Kwamatin M.D Abubakar ya bada shawarar a kori wasu ‘yan sanda 4, a ragewa 4 mukamai, sannan a daukaka darajar 7, haka kuma ya bukaci a sake fasalin masarautun gundumomi 17 na Jihar ta Zamfara.

Shugaban kwamatin M.D Abubakar, yaja hankalin gwamna Matawalle da yayi aiki da shawarwarin da kwamatin ya bayar domin samun dorewar zaman lafiya a Jihar ta Zamfara, inda daga bisani gwamna Matawalle ya godewa kwamatin bisa aikin da suka gudanar, kuma yasha alwashin yin aiki da shawarwarin kwamatin batare da yin kasa a gwuiwa ba, kamar yadda ya rantse yayin kama aiki, haka kuma zai tuntubi shugaban kasa dangane da wasu shawarwarin da kwamatin ya bayar wadan da suka shafi gwamnatin tarayya.

Wannan kwamatin dai bai ambaci sunan wadanda ake zagi ba.

Qalubale@gmail.com

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started