Daga Muhammad Gambo Yobe:

Kwamandan rukuni na biyu a hukumar sojoji dake karkashin shirin “Operation Lafiya Dole ( Commander Sector 2 Operation Lafiya Dole), Burgediya Janar Ibrahim Sallau Ali ya Jagoranci aikin kona Motocin safarar kifi da aka kama makare da kifiye a Geidam.
Motocin da aka kona a sabon barikin soja dake birnin Damaturu, an kama su ne a Yankin Geidam cike da kifi wanda aka haramta shigowa da shi suna kokarin shiga da shi jihar Jigawa.

Da yake jawabi jim kadan kafin kona Motocin, kwamandan runduna ta biyu Operation Lafiya Dole, Burgediya Janar Ibrahim Sallau Ali yace sojojin bataliya ta 159 dake karkashin shirin Operation Lafiya Dole a yankin Geidam ne suka kama masu fasa kwabrin bandan kifin a garin Bukarti dake karamar hukumar Yunusari ranar Juma’a 4 ga watan Oktobar nan na 2019.
Yace ‘yan fasa kwabrin sun shigo da kifin ne daga Diffa dake Jamhuriyar Nijar inda suke kokarin shigar da kifin da aka haramta shigowa da shi cikin jihar Jigawa a Nijeriya.


Burgediya Sallau ya kara da cewa kona wadannan motoci tare da kayan dake cikin su wani yunkuri ne na kawo karshen Boko Haram yana mai cewa wadannan kifaye na Boko Haram ne kuma da kifin ne Boko Haram ke yin ta’addanci da tada husuma a yankin Arewa maso gabas.
Daga Karshe ya gargadi dukkan al’umma da a guji sana’ar fasa kwabrin bandar kifi domin rundunar sojin dake Operation Lafiya Dole ta haram ta hakan a yankin arewa maso Gabas.
Ya kuke Kallon Matakin?
MAJIYA: Jaridar Dimokradiyy
Qalubale@gmail.com
