Daga Umar Faruq Muhammad:

Jiya nayi rubutu dangane da yadda wani Jami’in Karota yakamana batare da laifin sabo doka ba, har kuma aka cini tarar #5000 daga ofishin su.
A jiyan dai da yamma bayan nayi rubutun sai nasamu kiran waya daga bakuwar lamba, mai kiran yagabatar min da Kansa a matsayin Mal. Jamilu Dambatta, shine Babban Jami’in dake kula da Ofishin Karota na filin Eidi, yatambaye ni abinda yafaru, yakuma ce yana son gani na a ofishin nasu.
Yau naje mun hadu, yakarbe ni cikin Mutuntawa, tare da tattaunawa kan lamarin yakuma bincika yafahimci gaskiya ta da kuskuren Yaron sa.
Wannan lamarin yaburge ni matuka, ganin yadda yake bin diddigin lamari ya tabbatar da gaskiya yakuma zartar da hukunci, kafin ni naga wasu Mutane biyu da yasaurari Korafinsu, kuma yayi hukunci na Gaskiya, nima an hukunta dawo min da Nairori na, wadanda kuma ta bayyana sun taka doka an zartar musu da hukuncin tara.
Nasamu labari wannan ne Umarnin da MD Jan Zakara yabawa Wakilansa masu rike da cibiyoyin Karota, naga hakan a aikace wajen Jamilu Dambatta.
Ina kira ga duk wanda yaga an masa ba daidai ba ya garzaya wajen Jagororin Karota, da zarar an bincika suna bawa Mai Gaskiya hakkin sa.
Allah yakara basu ikon tsarkake aikin su.
Qalubale@gmail.com
