DA DUMI DUMINSA

Majalisar Dokokin Jihar Kano a zamanta na yau litinin 16/3/2020, ta dakatarda yan majalisun kananan hukomin hukumomi kamar haka;

1 Rt. Hon. Isyaku Ali Danja (PDP) Minority Leader (Gezawa Constituency)
2 Hon. Salisu Maje Ahmad Gwangwazo (PDP) (Municipal Constituency)
3 Hon. Labaran Abdul Madari (APC) (Warawa Constituency)
4 Hon. Muhammad Ballo Butu-Butu (APC) (Rimin Gado/Tofa Constituency)
5 Hon. Garba Ya’u Gwarmai (APC) (Kunchi/Tsanyawa Constituency)

Dakatarwar zata dauki tsawon wata shida ba tareda sun shiga majalisa domin wakiltar alummarsu ba. Majalisar kafin yanke hukuncin, ta zargi yan majalisun da tada rigima daidai lokacinda ake zama kamar yadda aka saba.

Idan ba’a manta ba satin daya gabata hargitsi ya tashi tsakanin yan majalisar a lokacinda mataimakin shugaban majalisar ya tashi domin neman sahalewar yan’uwansa akan karanta rahoton tuhuma da ake yiwa Mai martaba Sarki Muhammad Sanusi II mai murabus, wanda hakance ta fusata wasu daga cikin yan majalisar har zaman ya gagara a wannan rana.

Qalubale@gmail.com

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started