YAKAMATA GIDAJEN REDIYO SUYI GYARA

Daga Umar Faruq Muhammad

Yanzu nake karanta rubutun Mal. Asim Kurawa gameda yadda wani gidan Rediyo yabada labarin Fyade ga wata Yarinya tareda sanya sautin Yarinyar tana fayyace yadda abin yafaru, Yayi rubutun ne don bayyana Illar da Kafafen Labarai ke yadawa da sunan bada Labari.

Nadade ina jin takaici irin yadda Gidajen Rediyo musamman masu zaman Kansu ke azarbabin yada munanan Labarai, magana ta gaskiya akwai kusakurai sosai a yanayin yadda suke yadawar.

Idan mukayi la’akari zamuga yada labaran basa taka rawa wajen kaucewa barnar da akayi sai dai ma tazama kamar koyarwa ga wasu.

Akwai wata kafar Labarai data bada labarin wani Dan Sahu da ya gudu da kayan wasu Mata wanda a karshe Yan sandan Naibawa suka kamashi sakamakon lambar mashin din sa da Daya daga Matan ta haddace, abin mamaki a satin sai ga sabon labarin wani Dan Sahun shima yagudu da kayan wani.

Magana ta Gaskiya yawan yada munanan Labarai sukan zama kamar koyarwa ne ga wasu masu sauraren.

Idan kana bibiyar Gidajen Rediyon mu zakaga kamar Gasa suka dauki harkar Labarai ta irin usulubin dasuke yin Labaran, shiyasa basu fiye la’akari da sakamakon abinda suke yadawa zai haifar ba.

Munada kwararrun Matasa a Gidajen Rediyo, kuma sunada Ilmin Addini daidai gwargwado, ina fata zasu kara dagewa wajen bada shawarwari ga Gidajen su don kaucewa Yada Fasadi.

“KADA KUYADA BARNA A BAYAN KASA”

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started