Daga Bello Muhammad Sharada:

Kusan wata guda da ya gabata, gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci shugaban kasa Muhammad Buhari a fadarsa ta Aso Rock. A lokacin da ya kai masa wannan ziyarar ya yi guzuri da hoton sabon tsarin zane na 3D na zanen sabuwar gadar da yake niyyar gina wa a babban shatale-talen gidan mai na NNPC da yake unguwar Hotoro. Wannan randa shi ne mahadar Kano da jihohin da ke makwabtaka da ita ta kudu wato Jigawa da Bauchi har ya dangana da Yobe da Borno. Babbar hanya ce, mai daukar fasinja da kaya.
Gina gadoji a kwaryar birnin Kano yana cikin ayyukan da suke sanya annashuwa ga gwamnan Kano Dokta Abdullahi Ganduje. Yana alfahari da gadojin. Yana daukarsu da muhimmanci. Har ta kai ana yi masa kirari da “Architect of Modern Kano”. Manufar Ganduje a wannan aikin shi ne a rage cunkoso, a saukaka sufuri, a buda wajen harkar kasuwanci don a inganta harajin cikin gida. Wannan shi ne lissafin zahiri, tunanin badini kuma sai shi gugan karfen na Goggo.
A cikin shekara 40 da suka gabata Marigayi Air Commodore Hamza Abdullahi, gwamnan soja na Kano a mulkin Manjo Buhari shi ne ya fara yin gadar sama don masu tsallake titi. Gadar da ya yi ta karfe ce, kuma an yi ta a kan titin Asibitin Murtala. An yi wannan gadar a 1985-86. Kara habaka da yawan jama’a da ababen hawa tun wancan lokaci yana damun Kano kuma wajibi ne hukumomi su duba bukatar hakan don daukar matakin da ya dace. A shekarar 2012 ne tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya fara gina gada. Shi a hikimarsa yana so ya magance wahalar da mahaya ke fuskanta a mahadar Kabuga da Gadon Kaya da Gidan Murtala da Batar Sabon Gari. Wannan shi ne bayanin da gwamnati ta yi wa jama’ar gari.

A lokacin da Injiya Rabiu Musa Kwankwaso da mataimakinsa Dr Abdullahi Ganduje suka karbi mulki daga soja a hannun marigayi Kanar Aminu Isa Kontagora, daga 1999-2003 ya yi aikin fadada tituna na Birnin Kano da fasa wasu hanyoyi don su bulle kuma su hade da manyan titunan Kano kuma su bunkasa kasuwanci da sufuri. Wannan shiri shi ne “Urban Renewal Program” wanda aka gudanar da shi a karkashin kulawar Arch Aminu Abubakar Dabo
Akan aikin Kwankwaso Mallam Ibrahim Shekarau ya dora ayyukan gwamnatinsa na “Kano Road Map” wanda ya fadada manyan titunan Kano daidai da na Abuja da Lagos. Ya yi titi daga farkon Zoo Rd har karshensa, ya sake fasalin titin BUK tun daga Kofar Kabuga har Gidan Murtala. Ya zarce da shi daga Gidan Murtala har masallacin Juma’a na Fagge. Ya dauko daga kofar Nassarawa har gidan Gwamna. Ya tashi wani daga Kofar Kabuga har zuwa El Duniya a Kantin kwari.
Bayan Kwankwaso ya dawo a karo na biyu, daga shekarar 2011-2015 sai ya fitar da tsarin gina gadoji. Ya yi Gadar sama a mahadar Gidan Murtala da Titin Obasanjo da kofar Gidan rediyo na Kano. Sannan kuma ya kirkiro Gadar Kasa a Kabuga da Gadon Kaya. Kwankwaso ne ya bada tunani da zanen Gadar Titin Panshekara zuwa Madobi.
Shekara biyu da ya gabata gwamnatin jihar Kano ta aza harsashin gina gadar kasa a mahadar titin Zaria rd da titin Zoo rd. Ana kashe naira biliyan hudu da motsi a wannan aikin. Kafin ya kai karshe zai ci biliyan shida.
Jimlar ayyukan gadoji da Ganduje ya yi na kasa sun zama uku. Daya a kan titin Madobi, daya a kan titin Katsina, sai kuma ta titin Zaria. Sannan kuma ga aikin gadar sama a Sabon Gari kan Murtala Muhammad Way. Ana kan yi sabuwar gada a Asibitin Murtala da Kantin Kwari. Yanzu kuma an bada kwangilar gina gada a NNPC Hotoro akan naira biliyan Tara. In an gama za a gina wata a mahadar da za ta dangana titin Filin jirgin sama na Aminu Kano da titin Katsina Rd.
Da ainihin abin da aka kashe da kiyasin kudin wadannan ayyukan a zamanin Kwankwaso da Ganduje ya doshi naira biliyan 100.Dukkansu babu aikin kasa da naira biliyan biyu.
Anan ne nake da magana. Naira biliyan 100 ba wasa bane. Babu laifi a kashe su, amma “kudi a kashe su ta hanya mai kyau” Aikin gadojin nan “Infrastructure Investment” ne, menene alfanunsa, idan aka kashe su, nawa ake saka rai da tsammanin su jawo na riba? Shin gina titunan yana rage cunkoso ko kuwa kawai ya kara wa Kano kwalliya ne ?
Abu na biyu, shin wannnan manyan ayyukan gadojin shi ne bukatar mutanen birni da akasarinsu ‘yan kasuwa ne da ma’aikata da mata da matasa? Da aka dauki kudaden mutanen karkara aka gina gadoji a birni, haka shi ne dabarar raya jama’ar karkara, wanda akasarinsu manoma ne da kananan ‘yan kasuwa?

A fahimtata wannan ayyukan gadojin ba shi ne bukatar mutanen birni da karkara ba. Da Kwankwaso da Shekarau sun buda hanyoyin Kano na shiga da fita. Babbar matsalar masu bin hanya ko a mota ko a babur ko A Daidaita Sahu shi ne gajen hakuri da karya doka. Wannan kuwa musiba ce babba, gina gada ba zai yi maganinta ba.
Da Aliko Dangote da Bill Gate da Halifa Muhammad Sanusi II sun taba fada cewa Human Capital Development shi ne kashin bayan habakar kowacce kasa. Ma’ana gina ilimi da lafiya da muhalli da samar da aikin yi. Gina gadoji yana zuwa ne daga bisani.
Gwamna Ganduje zai iya ciwo ba shi mai kauri, ya kashe, amma fa a duba ayyukan da suke zasu gina jihar in an yi shi. Wannan kwalliya da kyale-kyale ba sa dorewa, saboda kayan yayi ne. Nan da wani lokacin kankani zamani zai zo a rushe su, a manta da kwalliyar, ginshikin da zai tabbata shi ne wanda aka gina shi na raya dan adam. .

Kano garin kasuwanci ne da noma. Kano gari ne mai albarkar jama’a da damarmaki masu tarin yawa. Me Ganduje ya yi a noma da kasuwanci da sana’a? Ina aka kwana a tashar jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano? Ina aka kwana a habaka tashar tashi da saukar jirgin sama? Ina aka kwana wajen gina Dala Inland Dry Port? Ina aka kwana da Export Processing Zone na Panisau? Ina aka kwana da samar da lantarki a Sharada da Challawa da Bompai Industrial Zone? Ina aka kwana da maganar habaka Commercial da Private Property Development a Kumbotso da Dawakin Kudu da Ungoggo da Gezawa da Madobi?
Ta yaya za a kashe kusan naira biliyan 100 a harkar gina gadoji, amma makarantun firamare da sakandire sai dada lalacewa suke yi? Ilimi ya zama banza a wulakance? Ta yaya sauro da kuda sun gagari kundila?
Ni ban gamsu da ayyukan gada ba. Wannan shi ne fahimtata . Bana goyon bayan cogen gina jiha ta hanyar North Korean Style, na fi gamsuwa da hanyar gina jiha ta hanyar South Korean style.
