Hukumar Fansho Ta Jihar Kano Na Bin Hukumomi Bashin #53bn

A wani gangamin taro da kungiyar fansho ta Jihar Kano ta shirya a Karamar Hukumar Kumbotso, wanda ya gudana a dakin taro na Islamic Centre da yake a Panshekara ranar Alhamis 8 ga watan Yuli, 2021

Shugaban kungiyar ya koka ta bakin mataimakinsa Alh Shu’aibu Musa Jibrin, masamman yadda ‘yan Fansho ke korafe-korafen rashin kula da hakkokinsu bayan ajiye aiki da sukayi, duba da cikarsu shekaru 35 suna aikin gwamnati kokuma cikarsu shekaru 60 da haihuwa.

Sha’aibu Musa Jibrin ya koka da yadda hukumomin gwamnati kimanin guda shida ke jan kafa wajen kin sauke nauyin da ya rataya a kansu kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta Fansho ta bayyana.

Dokar ta bukaci dukkanin ma’aikatun gwamnati su turawa hukumar ta Fansho kashi 8% da ake kwashewa daga albashin ma’aikatansu, sannan kuma su hada da kashi 17% na kason gwamnati na dukkanin yawan ma’aikatansu, su turawa hukumar Fansho

Wannan shine abinda ke gagarar ma’aikatun gwamnatin a Jihar ta Kano, inji Sha’aibu Musa Jibrin – ya kara da cewa yau kimanin shekaru 5 kenan hukumar Fansho ba ta iya biyan garatuti ga wadanda su ka bar aikin, gashi kuma ya fara shafar kudaden Fansho.

Shugaban ya ce dole ce tasa suka bude asusun ajiya guda biyu, daya na ‘yan Fanshon Jihar daya kuma na ‘yan Fanshon kananan hukumomi, domin zalincine ka dauki kudaden wadanda ke biyan kudadensu ga hukumar ta Fansho ka biya wadanda suke kasa biyan kason da ya wajaba a kansu.

Shine dalili da wasu ma’aikatan kananan hukumomi suke ganin an yanke ma su kudadensu na Fansho, wannan ya biyo bayan rashin turawa da kason kudaden da ma’aikatansu keyi ga hukumar ta Fansho.

Zuwa yanzu, hukumar Fansho ta jihar Kano na bin bashin hukumomin gwamnati kudaden da su ka kasa zubawa a aljihun hukumar Fansho fiye da zunzurutun kudi Naira biliyan Hamsin da Uku (#53bn)

Ita kuma hukumar ta Fansho zata iya biya dukkanin hakkokin garatutin ‘yan Fansho ne cikin kwanciyar hankali, idan ta mallaki Naira biliyan ashirin da bakwai zuwa da takwas (#28bn) a ta bakin Shugaba – Sha’aibu Musa Jibrin

Ya kara bayyana cewa, ko layi za’a ja, matukar kowace hukumar gwamnati zata biya kason da doka ta bayyana, ko shakka babu za’a rage wahalhalun da ‘yan Fanshon ke fama, duba da tsadar rayuwa, inda yace hukumar SUBEB da Min for LG sune ke kan gaba wajen rike kudaden

Hukumar Fansho na bin SUBEB fiye da Naira biliyan Talatin da Uku (#33bn) inda Hukumar Min for LG ke biye da bashin fiye da Naira biliyan Goma sha Daya (#11bn) inda Jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil, Wreca, Water Board da Internal Revenue ake binsu fiye da (#9bn)

Sha’aibu Musa Jibrin yayi kira ga hukumomin gwamnati su dubi Allah su sauke nauyin da Allah ya dora a kansu, domin kuwa duk ma’aikaci karshensa dai hukumar Fansho, idan ta gyaru kazo ka iske ta lfy, idan ta back kaima ka shiga cikin masu kokawa.

Daga karshe yayi addu’ar Allah yai wa shugabanninmu jagora, ya basu ikon sauke nauyin da ke kansu, Allah ya taimaki yan Fansho ya fito ma su da hakkokinsu tun suna raye, ya roki Allah wadanda su ka mutu cikin bakin cikin wannan yanayin Allah ya gafarta ma su.

qalubale.news.blog

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started