Yanzu na samu labarin Shugaban kasa Muhammad Buhari ya aika wa majalisar kasa takardar cewa ba zai sa hannu akan sabuwar Dokar Zabe ta 2021.

Sai da shugaba Muhammad Buhari ya yi kwana talatin cur sannan ya mayar da amsa ga majalisar kasa kan sabuwar dokar zabe ta “Electoral Bill 2021”
An yi ta nuku-nuku da kumbiya- kumbiya, don a biya wa gwamnoni bukatarsu. Gwamnoni sun yi nasara, burinsu ya cika, mutanen Najeriya sun yi asara.
Alkawarin da PMB ya dauka zai bar gadon sahihin tsari na zabe da shugabanni ya fadi kasa warwas.
A tsaro mun fadi. A tattalin arziki mun fadi. A dimokuradiyya mun fadi.
Duk dalilai da shugaban kasa Muhammad Buhari ya dogara da su don fatali da wannan gyararriyar dokar, an gina su a gurguwar fahimta.
Wannan matsayin ya dada tabbatar min da cewa BA SAITI AKA ZO A YI WA NAJERIYA BA.
A’a an zo a more kuma a hole.
Daga Bello Muhammad Sharada
