
Talata 18 ga watan Janairu, Shugaban Kasar Najeriya Muhammad Buhari ya kaddamar da Dalar Shinkafa, wannan yana daga cikin kudurorin shugaba Buhari na samar da Kasa mai dogaro da kanta masamman ta fannin abinci.

Buhari ya kaddamar da Dalar Shinkafar ne a birnin Abuja inda kamfanoni masu zaman kansu mallakin ‘yan Najeriya su ka baje kolin irin shinkafar da suke samarwa domin ciyar da Kasa da kuma tabbatar da ‘yan Najeriya sun dogara da kansu wajen noma isasshen abincin da za’a dogara da shi batare da dogaro da kasashen ketare ba.

Abinda ya ragewa talakawa su gani shine, Gwamnati ta tsaya tsayin daka domin ganin abincin yana isa ga masu bukata a cikin Kasar, har sai ya wadaci jama’a kafin a fitar dashi ketare domin siyarwa.

Haka kuma Gwamnati ta sa idon ga masu yin simogal domin fitar da abincin kamar yadda ta sa Ido wajen shigowa da shi, a baya dai Gwamnatin ta ce, Fasakwaurin Shinkafa Haramun Ne yin hakan zai takaita ko ma ya hana tsadar da talakawa ke fama da ita a halin da ake ciki yanzu.
Allah ya ba shugabannin mu ikon yin amfani da irin wannan abinci da ake samar wa a Nageria a gidajen su.
