Yaushe Abba Kyari ya koma bakin aiki bayan an dakatar da shi

Harkar tsaro a Najeriya abar tuhuma ce – dalili na shine, kowa ya san an dakatar da Abba Kyari daga wannan aiki a hukunce, har zuwa wannan rana da muka buga wannan labari babu lokacin da wani ya ji cewa an maida shi bakin aiki a hukunce, wane dalili ne ya ba Abba Kyari damar komawa bakin aiki?

Wannan harkalla fa kamar yadda labarin ya zo, anyi ta ne daga watan Janairu zuwa wannan rana da muke buga wannan labari – ko dai akwai sa hannun wadanda bamu gani da idanuwan mu a wannan harkalla – order from above?

Yaushe Abba Kyari ya koma bakin aiki bayan an dakatar da shi, har ya sami damar yin wata sabuwar harkalla?

A ra’ayin wasu mutane su na cewa, ta bayan fage ya koma bakin aikin nasa sakamakon yaransa har yanzu su na yin biyayya a gareshi kuma su na ba shi bayanan sirri na abinda ke faruwa a ofis – shi kuma yana basu shawarar yadda za su tinkari aikin nasu.

Hakane ko ba haka bane, ya rage bincike ya tabbatar kuma a sanar da jama’a yadda akayi Abba Kyari ya tafka wannan harkalla da sunan aikin da tuntuni aka dakatar da shi, ko kuma dai daga sama ne aka daure masa gindin yin aiki ta bayan fage, bayan kuma ga shugaban da ya maye gurbin sa amma ba’a yin aikin dashi – idan ba haka ba ne, me yasa su shugabanninin NDLEA su ka saurari wanda ba ya kan kujera domin yin wata alakar aiki dashi?

https://t.co/kKZ1ap66dZ

Radio BBCHausa sun riwaito cewa, shi Abba Kyari da ake tuhuma yayi magana da jami’an NDLEA a aikace kuma a hukunce, har ma ya bukaci jami’an NDLEA din su karbi masu laifi daga hannun su, ma’ana dai suyi handover kenan daga hukumar tsaro ta yan sanda zuwa ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi.

Idan wannan zarge-zarge sun tabbata, ko shakka babu an fara gano musabbabin abinda ya jawo rashin tsaro kenan a Najeriya – kamar yadda masana sukayi sharhi cewa, duk matsalolin tsaro a Najeriya ya samo asali ne ta hanyar sha da fataucin miyagun kwayoyi.

Qalubale

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started