Bayan shekaru bakwai, Ganduje ya dawo da biyan garatuti

Gwamnatin jihar Kano, karkashin maigirma Gwamna Ganduje, ta dawo da biyan garatuti, bayan wata yarjejeniya da ta cimma da shugabannin hukumar fansho ta jiha, cewa zata dinga bada wani kaso na kudin kowane wata domin a dinga ragewa tsoffin ma’aikatan hakkin su.

Tsarin biyan garatutin, kamar yadda shugabannin su ka tsara, duba da karancin kudin da yake hannu kuma ga yawan jama’a da su ke a kasa, shugabannin sun yanke shawarar biya daga inda aka tsaya tun a baya, wato shekarar 2016.

Haka kuma duk wanda kudin garatuti din sa bai haura miliyan biyu da rabi (#2.5m) ba, zai sami kudin sa gaba daya Insha Allah!

Wanda kudin sa ya haura (#2.5m) shine zai sami wani kaso na kudin, wato (part payment), shima kuma duk lokacin da za’ayi biya na gaba sunan sa zai sake fitowa har a gama biyan sa.

Muna addu’a Allah ya kiyaye tunanin gwamnati ta ci gaba da alkawarin da ta dauka na bada kudin duk wata-wata

Wadanda Allah ya sa su ka sami nasu, muna addu’a Allah ya sanya albarka a cikin kudin.

Qalubale

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started