BUHARI BA SHUGABA BANE — Bello Muhammad Sharada

Muna rokon Allah Ta’ala kada ya maimaita mana mulki irin na Buhari da Jonathan, Allah Ta’ala ya bamu jagora a kasa da jihohi 36 har Abuja da kananan hukumomi 774 masu alheri da za su tausaya mana, su kalli matsalolinmu, su yi bakin kokari wajen shawo kansu da magancesu.

“Rabbana akrijna min hazihil Qaryatil zalimi ahalulaha, wajaalanna min ladunka waliyyan wa jaalna min ladunka nasira.”

Jiya mahara, wato miyagun daji a kan babura kusan mutum 300 suka shammaci motocin rakiyar shugaban kasa akan hanya. Sun fito daga Abuja zuwa Daura, inda PMB zai yi hutu da shagalin salla. Suka bude musu wuta, a sanadin haka suka kashe mataimakin kwamishinan ‘yan sanda.

Jiya wajen karfe goman dare, wasu gungun mahara da adadi mai yawa suka fasa gidan kurkuku na Kuje da ke Abuja. Akwai furusuna 994 a ciki, da shiga sun tarwatsa fursunonin, har mutum 600 sun gudu. A cikin wadanda ake tsare da su har da gogaggun ‘yan Boko Haram ko ISWAP/Ansaru su 64.

A sati guda da ya gabata a jihar Neja a karamar hukumar Shiroro, shugaban kasa Muhammad Buhari yana kasar Portugal aka kaiwa sojan Najeriya farmaki aka kashe sojoji 30 da mobayil bakwai da yan bijilan. Haka shugaba Buhari yana kasar Spain aka kai hari coci a Owo ta Ondo aka kashe mutum 40. Tun daga watan Janairu 2022 babu watan da ya zo Buhari bai fita waje ba. Yana wajen kuma za a kashe tai, sai dai ya aiko da gaisuwa da ta’aziyya.

Abin takaici da Allah Wadarai duk da munin wannan ta’adda da aka yi jiya a Kuje da Dutsinma a Abuja da Katsina, amma shugaban kasa ya hau jirgin sama da tawaga ya tafi kasar Senegal. Zancen da muke yanzu ya kusa isa can.

Nan fa a Najeriya ana jimami, ana fargaba, ana sallallami, ana tashin hankali ko a jikin Buhari, to me zamu yi da Buhari, wallahi Buhari ba shugaba bane, kuma bama yinsa. Mun yi tir da halinsa da halin ko in kula da yake yi wa al’ummar kasar nan.

A da nakan ce, ministan tsaro Bashir Magashi da ministan cikin gida Abdurauf Aregbesola da National Security Adviser Babagana Munguno su yi murabus, su bar kujerunsu, abin takaici ne zamansu. Yanzu kamata ya yi ‘yan majalisar dattijai su tankado keyar Buhari tun lokacinsa bai cika ba ya fado. Su wurgo shi daga kan kujerar mulki, su hantsilo da shi, sai mu ga ta inda zai rika yawo a Kaduna ko Abuja ko Daura.

BUHARI BA SHUGABA BANE

Qalubale

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started