Zamfara: Hannun Sarakuna, Sojoji da ‘yan Sanda a tada kayar baya

Ana zargin sarakunan gargajiya 5 da masarautunsu na gundumomi 33 a Jihar Zamfara wajen hada baki da ‘yan tada kayar baya, kamar yadda majiyarmu ta tsegunta mana cewa, kwamatin da gwamna ya kafa domin nemo bakin zaren, karkashin wani tsohon shugaban ‘yan sandan Najeriya Alh. M.D Abubakar.

Kwamatin M.D Abubakar ya bada shawara a sauke sarakuna 5 da dagatai 33 da masu unguwanni, haka kuma yabada shawarar a tuhumi daya daga cikin sarakunan a kotu, sannan yayi kira ga gwamnatin tarayya ta kafa kotu ta masamman domin hukunta wasu sojoji 10 da aka samu da hannu dumu-dumu cikin wannan badakala.

Kwamatin M.D Abubakar ya bada shawarar a kori wasu ‘yan sanda 4, a ragewa 4 mukamai, sannan a daukaka darajar 7, haka kuma ya bukaci a sake fasalin masarautun gundumomi 17 na Jihar ta Zamfara.

Shugaban kwamatin M.D Abubakar, yaja hankalin gwamna Matawalle da yayi aiki da shawarwarin da kwamatin ya bayar domin samun dorewar zaman lafiya a Jihar ta Zamfara, inda daga bisani gwamna Matawalle ya godewa kwamatin bisa aikin da suka gudanar, kuma yasha alwashin yin aiki da shawarwarin kwamatin batare da yin kasa a gwuiwa ba, kamar yadda ya rantse yayin kama aiki, haka kuma zai tuntubi shugaban kasa dangane da wasu shawarwarin da kwamatin ya bayar wadan da suka shafi gwamnatin tarayya.

Wannan kwamatin dai bai ambaci sunan wadanda ake zagi ba.

Qalubale@gmail.com

OPERATION AUREN MATA HUDU DOLE

Daga Datti Assalafiy:

Duk wanda Allah Ya hore masa arziki da lafiyar da zai iya auren mata hudu ya rayu da su amma baiyi hakan ba saboda kwaikwayon tsarin mutanen banza ‘yan boko aqeedah, to gaskiya bai taimaki kansa ba, kuma bai taimaki al’ummah ba

Jama’a idan kuka duba halin da muke ciki yanzu, a kowani lokaci mata ninka maza suke a yawa, idan akace maza su rayu da mace daya sauran matan kuma su auri kansu kenan?

‘Yan boko aqeedah idan za’a biye ta tasu auren ma ba za’ayi ba, sai dai Zina da Luwadi da Madigo, don su a gurinsu wayewa ne, ba zaka taba rasa ‘yan boko aqeedah da dabi’ar Zina da Luwadi ba, sai kalilan daga cikin wadanda ba su rika a kidar ba

Yanzu munkai matsayin da ba’a iya banbance tsakanin ‘yan mata da zawara su wa sukafi yawa? idan za’a auri ‘yan mata kadai a kyale zawarawa, mazan zasu kare, zawarawa ba su samu masu auren su ba

Yau inda ace masu hali zasu dinga auren mata hudu to da sun taimaki al’ummah ta fuskoki da dama, zai rage sabon Allah, lalata da fasadi, zai rage yawan ‘yan mata da zawarawa da suke gaban iyayensu babu mijin aure, sun zama tamkar kishiyoyi a gurin wadanda suka tsuguna suka haifesu, kullun fada, uwa tana jinin al’ada ‘yar ta tanayi, kunga abu ai baiyi tsari ba

Don Allah jama’a masu karfin hali da lafiya ku fara tunanin taimakon al’ummah ta hanyar auren mata hudu, ga nan ‘yan mata birjik suna jiran mijin aure, sun rika har sun rike a gaban iyayensu

Ina rokon Allah Ya mana albarka, Ya bamu ikon auren mata hudu da abinda zamu iya rikesu da shi Amin

Qalubale@gmail.com

Babu lokacin da ma’aikata zasu fara karbar sabon tsarin albashi

Kungiyar kwadago tace ya zuwa yanzu babu lokacin da ma’aikata zasu sa rai da fara karbar sabon tsarin albashi na kasa baki daya.

Wannan ya biyo bayan komawa da hannun agogo baya da gwamnatin tarayya tayi na sake fasalin kwamitin da ta nada domin daidaitawa da gamammiyar kungiyar kwadago ta kasa.

Fiye da watannin shifa (6) da suka wuce majalisar tarayya ta amincewa gwamnatin tarayya ta biya mafi karancin albashin na Naira dubu talatin (#30.000) ga ma’aikatan kasarnan baki daya, bayan an shafe fiye da shekara daya (1) ana fafatawa wajen nemo yawan albashin da yafi dacewa ga ma’aikatan, daga baya kuma shugaba Buhari ya sa hannu a fara biya.

Abin mamaki duk da wannan lokaci da aka shafe na kusan shekaru biyu (2) da tattaunawa da sahalewar majalisa da sahalewar shugaban kasa amma abin yaci tira, domin har yanzu ma’aikata na dandana wani salon mulki na yaudara a hannun wannan gwamnati, inda shugabannin kwadago suke cewa tunda suke basu taba ganin irin wannan mulkin mallaka da yaudara ga ma’aikata ba sai a wannan karo.

Babban abin lura shine, yan kasuwa tunda fari da sukaji za’a karawa ma’aikata albashi suka karawa kayayyakin masarufi na yau da kullum kudi kuma har zuwa yanzu kudaden kayayyakin sai kara karuwar sukeyi.

Muna fata Allah ya kawo karshen gasawa ma’aikata aya a hannu da gwamnatin Najeriya keyi.

Qalubale@gmail.com

Zamu cigaba da rufe iyakokin Najeriya har sai mun cimma yarjejeniya

Shugaban hukumar kula da fasa kauri Col Hameed Ali (mai ritaya) ya bayyana cewa, Najeriya zata cigaba da rufe iyakokin kasar, har sai lokacin da aka bi ka’idojin shige da ficen al’umma da kayayyaki kamar yadda kungiyar kula da tattalin al’ummar Afrika ta yamma (ECOWAS) ta tsara.

Hameed Ali yayi wannan bayani ne a lokacin da yake zagayen kan iyakokin kasar a kan iyakar Idiroko ta Jihar Ogun, yace babu alama kawo karshen rufe kan iyakar a nan kusa har sai an cimma wannan yarjejeniya.

Hameed Ali yana tare da shugaban hukumar shinge da fice ta kasa Muhammad Babandada yayin wannan ziyara.

#SenIbrahimShekarauMedia

MAGOYA BAYAN KWANKWASO SUNYI YUNKURIN HALLAKA MINISTA A NIGERIA

Daga Fa’izu Alfindiki

Abinda wasu ‘yan daba daga cikin darikar Kwankwasiyyah suka yiwa Ministan Sadarwa a Nigeria Dr Isah Ali Ibrahim Pantami jiya a filin jirgin sama na Kano yunkurin kisa ne, imba don Allah Ya kaddara jami’an tsaron da ke rakiyarsa sunyi bajinta ba wajen bashi kariya watakila da yanzu wani labarin ake na dabam.

Za’a iya tuna watannin baya lokacin da wasu ‘yan daba daga cikin magoya bayan darikar Kwankwaso suka tabbatar wa duniya cewa zasu hallaka Malam Isah Ali Pantami tun kafin ya zama Ministan Sadarwa lokacin yana matsayin Darakta Janar a ma’aikatar NITDA a tsakiyar Azumin watan Ramadan da ya gabata, sai gashi a jiya sun tabbatar mana da yunkurin kashe shi din.

Sannan sunyi kokarin su keta masa mutunci ta hanyar cire masa hula da kayan jikinsa su masa tsirara bayan jifar da suka masa da ihu da tsinuwa sai Allah Ya kubutar dashi.

Muna cike da tsoro idan basu saka wa Maigirma Minista guba (poison) ba saboda sun samu sa’ar taba jikinsa, akwai killer poison ko killer cancer disease wanda ‘yan leken asiri (spy) suke amfani dashi su saka a jikin mutumin da suke so su hallaka cikin kankanin lokaci ba tare da an gane su ba, don haka ko da wasa mu ba mu yarda da mamayar da ‘yan dabar Kwankwasiyya suka yiwa Ministan Sadarawa ba, dole ayi bincike.

A cikin birnin Kano wannan mummunan al’amari ya faru, don haka muna kira ga gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta da dauki matakin gaggawa wajen zakulo mutanen da suka jagorancin yunkurin hallaka babban mutum a tsarin dokokin gwamnatin Nigeria Maigirma Ministan Sadarwa don su fuskanci hukunci ko da sun kasancewa daga cikin wadanda aka tura Indiya ne a dawo da su gida a hukuntasu.

Sannan muna kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar daukar matakin gaggawa akan darikar Kwankwasiyya, don kiyaye faruwar abu makamancin wanda suka yiwa Maigirma Ministan sadarwa, babu shakka da sun samu sa’a hallakashi zasu yi.

Muna rokon Allah Ya cigaba da tsare mana rayuwar Dr Isah Ali Ibrahim Pantami daga dukkan sharri Amin.

Qalubale@gmail.com

Shari’ar Zaben Gwamnan Kano

Daga Bashir Abdullahi El-bash

SHARI’AR ZAƁEN GWAMNAN KANO, JAM’IYYAR PDP DA ABBA GIDA-GIDA, SUN GAZA WAJEN GABATAR DA INGANTATTUN HUJJOJI A KOTU

Daga Bashir Abdullahi El-bash

Ta faru ta na kuma daf! Da ƙarewa, domin kuwa yanzu haka kotun da ke sauraren ƙararrakin zaɓen gwamna a Jihar Kano, ta kammala sauraro da tattara bayanai da hujjojin ɓangaren masu ƙara, (jam’iyyar PDP) da ɗan takararta na gwamna, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) da kuma ɓangaren da aka yi ƙara, jam’iyyar (APC) da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Mai shari’a Halima S. Ibrahim ita ce ta jagoranci tawagar alƙalan da su ka zauna kan shari’ar, ta kuma bayyana cewa nan gaba kaɗan za a sanya ranar da kotun za ta yanke hukunci.

Shi dai lauyan jam’iyyar (APC) Alex Inzinyon (SAN) ya bayyana cewa, “jam’iyyar PDP ta yi zargin tafka maguɗi ne, amma kuma ta gaza gabatar wa kotu sahihan hujjojin da ta dogara da su wajen shigar da wannan ƙara.

A ya yin kuma da lauyan jam’iyyar ta (PDP), Abba Kanu Agabi (SAN) ya bayyana cewa sun yi imani Abba Kabir ne ya lashe zaɓe a zagayen farko, kuma wannan ita ce babbar hujjarsu.

Sai dai kuma, lauyan hukumar (INEC), Ahmad Raji (SAN), ya bayyana cewa duk wata dama da jam’iyyar (PDP) da Abba Kabir su ka nemi a ba su wajen bincike an ba su, amma duk da haka sun gaza wajen bayar da gamsassun hujjojin da za su gaskata iƙirarin da su ke a kotu. Da wannan ne ma ya buƙaci kotun da ta yi watsi gami da fatali da wannan ƙara gaba ɗaya.

Qalubale@gmail.com

Masu amfani da sim card wajen aikata laifuka sun shiga uku

Daga Datti Assalafiy:

MASU AIKATA LAIFUKA TA HANYAR YIN AMFANI DA LAYUKAN KIRAN WAYA (SIM CARD) SUN SHIGA UKU

Maigirma Ministan Sadarwa na Kasarmu Nigeria Ash-sheikh Dr Isah Ali Ibrahim Pantami ya bayyana cewa mutanen da suke amfani da layukan kiran waya wajen aikata miyagun laifuka za’a fara bin diddiginsu a tsakanin awa daya kacal a kamasu

Maigirma Ministan ya bayyana haka ne jiya Litinin a garin Katsina lokacin da ya wakilci Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari wajen kaddamar da National Emergency Toll-Free Number (112), da kuma Katsina State Emergency Communications Center wanda aka gina domin habbaka harkan sadarwa a Nigeria

Maigirma Ministan ya kara da cewa za’a gina cibiyar Emergency Communications Centre a jihohin Nigeria 36, babu wani kuduri da ma’aikatar sadarwa zata kaddamar imba kudirin shugaba Buhari ba wajen habbaka harkan sadarwa, tattalin arziki, da yaki da cin hanci da rashawa da tabbatar da tsaron rayukan ‘yan Nigeria

Maigirma Minista ya tabbatar da cewa nan da awanni 48 za’a rufe duk wani layin waya da ba’a yiwa rijista ba

Muna rokon Allah Ya taimaki Ministan Sadarwa Ya cika masa dukkan burinsa na alheri

Qalubale@gmail.com

Jagoranci abin misali

Daga Shamsuddeen Hamisu Maishinku 23/9/2019

Tabbas Abun da Governor Malam Nasir El-Rufai Na Kaduna yayi Abune Maikyau Na Sanya dansa A Makarantar Gwamnati dayayi,

Kuma haka yadace Shugabannin mu Sudunga yi domin inganta ilimi.

Amma Sai kaga Malaman Makaranta Ma Na Gwamnati Basa Barin ‘Ya’yan su Suyi Karatu, A Makarantar Gwamnati.

Tayaya ilimi Zaigyaru?

Qalubale@gmail.com

YAWAN JAMA’A MASU AMFANI SHINE ABIN ALFAHARI

Daga Comrade Auwalu Mudi Yakasai.
Juma’a 22/09/2017.
(Juma’a, 1 Muharram 1439 AH).

A shekarun baya an san al’ummar Hausa/Fulani a ko ina a duniya wajen juriya da jarumtaka da gaskiya da rikon amana da sadaukar da kai wajen gwagwarmayar neman halak da neman ilimi dadai sauran halaye masu kyau.
Abin takaici a yanzu da muka kara yawa sosai kuma muke bukatar irin wadancan halaye masu kyau sai abin ya canja.
A yau wasu daga cikin mu sun shahara wajen girman kai da son zuciya da lalaci da karya da kyashi da alfahari da hassada da cin amana.
Wasu daga cikin matasan mu babu abinda suka iya sai tumasanci da fadanci da kwadayi da munafurci. Babban abin haushin ma sai ka ji matashi yana alfaharin cewa shi ya fi karfin yayi wata karamar sana’a ko da kuwa da ita mahaifinsa ya rayu, kuma ita aka gada a gidansu. Amma wannan kuma bai hana shi yawon roko da maula a wajen masu irin wannan sana’ar ba.
Sakamakon haka duk sana’oi da aka san mu da su a gidajen mu kusan duk sun durkushe, wadansu ma an daina su baki daya, wanda hakan ya kara haifar mana da talauci da zaman banza.
Duk wanda ya zagaya Najeriya sosai zai fahimci cewa a yanzu matasan mu kadan ne suke iya fita sauran jihohi neman halak dinsu. Mafiya yawan matasan mu suna zaune ne a lunguna babu abinda suke sai surutan banza da musun siyasa da zargin cewa wai ba a taimaka musu kawai saboda mutuwar zuciya da son banza. Wasu daga cikinsu ma har sukan shiga shaye-shaye da bangar siyasa da sace-sace dadai sauran dabi’u marasa kyau, maimakon su maida hankali wajen neman ilimin addini da na zamani wadanda zasu taimake su a nan duniya da kuma lahira. Wadansu kuma ma iyayensu da yayyensu ne abokan gabarsu kawai saboda suna kokarin nuna musu gaskiya. Babu biyayya da ladabi ga iyaye ballantana ma a kyautata musu.
Wani abin al’ajabi ma shine yadda zaka ga matashi kai kana jin tausayin sa, amma shi kuma yana jin haushin ka. Kullum burinsu shine su sami kudi su more rayuwa duk da yake basu dauko hanyar da zata kaisu ga hakan ba.
Babu shakka matukar muka ci gaba da zama a irin wannan hali na rashin sanin ya kamata, to tabbas zamu cigaba da rayuwa cikin damuwa da koma baya da talauci da rashin zaman lafiya.
Gaskiya ne muna da yawa kwarai da gaske. Amma yawan namu ba zai amfane mu ba sai mun jajirce wajen dora rayuwar mu akan tafarki madaidaici.
Lokaci yayi da zamu farka mu yi amfani da yawan da muke da shi don mu amfani kanmu da al’ummar mu.
Wajibi ne kowannen mu babba da yaro da mai arziki da talaka da shugabanni da mabiya da malamai da almajirai kowa ya gyara zuciyar sa kuma mu kyautata niyya a dukkan al’amuran mu idan har muna son Allah (SWT) Ya dube mu da idon rahama.
Allah (SWT) Ya sa mu gane gaskiya, Ya kuma bamu ikon bin ta.

Qalubale@gmail.com

Taya murna ga sarakunan Kano

Daga Ahmad Mohd Gona:

Muna taya sarakunan Kano murna bisa samun Lambobin girma

Aminu Ado Sarkin Bichi shine Mai daraja ta daya (1) yayinda shikuma Sunusi Lamido aka Kara masa Lamba ya koma mataki na biyar (5) .

Qalubale@gmail.com

SOJOJI SUN HALLAKA MANYAN KWAMANDOJIN BOKO HARAM/ISWAP GUDA BAKWAI

Daga Datti Assalafiy:

Rundinar sojin hadin gwiwa na kasashen dake iyaka da tafkin Chadi Multinational Joint Task Force (MNJTF) sun samu nasaran hallaka wasu daga cikin manyan kwamandojin yakin kungiyar Boko Haram/ISWAP reshen ISIS na duniya

Wannan nasara ta biyo bayan ruwan wuta da dakarun sojin hadin gwiwar sukayi ta sama da jiragen yaki da kuma sojojin kasa ‘yan kundunbala a wani katafaren yanki da ake kira Tumbus dake tafkin Chadi, wanda yayi sanadin hallakar ‘yan ta’adda masu tarin yawa da kwamandojin yakin su

Sahihan bayanai ya nuna cewa wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun tsallaka sun gudu zuwa kasashen Sudan da Kasar Afirka ta tsakiya, sannan manyan kwamandojin yakinsu a kalla guda 7 suka hallaka sakamaon ruwan wuta da dakarun sojin sukayi ta sama da kasa

Ga sunayen manyan kwamandojin yakin Boko Haram/ISWAP da suka hallaka kamar haka
1-Abba Mainok
2-Bukar Dunokaube
3-Abu kololo
4-Abor Kime ( balarabe ne ‘dan kungiyar ISIS da yake bawa Boko Haram/ISWAP horo).
5-Mann Chari.
7- Dawoud Abdoulaye (‘dan Kasar Mali)
7- Abu Hamza.

Wadannan kwamandojin ‘yan ta’adda da aka hallaka sune suke lura da ayyukan ta’addanci a yankin Tumbus dake tafkin chadi, ba lallai ne ya zama asalin sunayensu ba, amma shine sunan da ake musu lakabi dashi a yankin, rundinar sojin tana kokarin tattara dukkan bayani a kansu

Wannan sanarwan ya fito a yau juma’a 20-9-2019 daga mukaddashin mai magana da yawun rundinar sojin Nigeria Kanar Sagir Musa

Allah Ka kara tabbatar da nasara akan ‘yan ta’addan Boko Haram

Qalubale@gmail.com

Fasakwaurin Shinkafa Haramun Ne

Daga Yasir Ramadan Gwale
16-09-2019

Sumogal din shinkafa da ake yi da babura ko fasakwaurinta daga kan iyakokin Nijeriya zuwa cikin gida Haramun, kamar yadda hukumar dake kula da wannan janibi ta sanar. Mutane da yawa na sukar wannan lamari, watakila bisa son rai ko kuma bisa jahilci.

Hakikanin gaskiya yana da kyau mutane su fahimci cewar, manufofin wannan gwamnatin inganta tare da habakar harkar noma musamman na shinkafa, domin manoman shinkafa na gida su samu arziki, ‘yan Najeriya su ciyar da ‘yan Najeriya da shinkafar da aka noma a cikin gida.

Wannan na daga cikin manufofin Gwamnatin Buhari kan bunkasa harkokin noma a Najeriya. Wannan ya sanya hukumar kwastan ta kasa sanya dokoki da ka’idoji kan batun shigo da shinkafa zuwa Najeriya daga kasashen waje.

Hukumar kwastan, tace yin sumoga ko fasakwaurin shinkafa ta kan iyakoki haramun ne, saboda hujjojin da shugaban hukumar Hameed Ali ya bayar, domin kudin da gwamnati ya kamata ta samu na harkar futo, anyi mata asararsu, sannan an shigo da abinda ake zargi yana dauke da guba.

Na farko ita wannan shinkafa da ake shigo da ita Najeriya ta barauniyar hanya, dauke take da guba, domin kafin isowarta Najeriya, an zuba mata sinadarai iri iri wanda zasu hanata rubewa ko lalacewa, saboda warin ruwan teku da ruma da kuma kumewa, wanda binciken hukumar kwastan ya tabbatar da cewar wannan shinkafa mai dauke da wadannan sinadarai tana cutarwa ta hanyar sanyawa mutane ciwon kansa.

Ciwon kansa ko sankara, ba ciwo bane da ake dauka nan take, watakila sai bayan wasu shekaru ciwon ke bayyana a jikin masu dauke da shi. Da wannan dalili da ma wasu, hukumar kwastan tace, duk wanda zai yi kasuwancin shigo da shinkafar waje zuwa Najeriya, to, ya shigo da ita ta hanayoyin da suka dace, domin a yi mata gwaje gwaje a tabbatar da inganci da kuma lafiyarta. To meye laifin hakan?

Mu ‘yan Najeriya muna da al’adar rashin girmama duk abinda muke da shi. Tayaya manomanmu zasu samu cigaba a harkar noman shinkafa alhali muna kaucewa sayan ‘yar gida muna cin wadda ake shigo da ita daga waje wadda ke dauke da sinadaran da ka iya illata jiki?

Ba daidai bane, mutane su dinga wasa da ratuwarsu, akan dan abinda za a basu in sun yi sumoga din shinkafa daga kan iyakokin da aka rufe zuwa gida Najeriya. Gwamnati dole ta karewa al’umma jini da dukiya da kuma mutuncinsu.

Me yasa masu kasuwancin shinkafa suke son lallai sai dai su shigo da ita ta barauniyar hanya, ta hanyar yin sumoga ko fasakwaurinta? Alhali Kuwa akwai yadda zasu iya shigo da ita a bisa tanade tanaden hukuma, ta anyar mfania da gabar tekun ad gwamnati ta ware domin yin harkar futo.

Yana da kyau ‘yan Najeriya su yiwa kansu tambayar me yasa ake sumogal din shinkafa indai sahihiya ce, kuma halastaccen kasuwanci mutane suke yi na sayar da shinkafar? Indai sun tabbatar shinkafar bata dauke da guba, me yasa ake tsoron shigo da ita ta gabar teku?

Ya danganta, ko dai ace zata yi tsada idan aka shigo da ita ta kan iyakokin Najeriya da aka tanadar wato teku, wannan kuma ba wani abin damuwa bane, domin wanda ba shi da ikon cin shinkafar da aka shigo da ita daga waje saboda tsada, yana iya sayan wadda aka noma ta a Najeriya, kuma wannan shi zai baiwa manoman shinkafa na gida damar bunkasa harkar noman shinkafar gida.

Babu wata gwamnati da ta san abinda take yi, zata yadda a dinga jidar dala daga Nijeriya, ana zuwa wasu kasashe ana azurta manoman shinkafar can kasashen, suna bamu shinkafar da aka cika ta da sindaran da zasu illata lafiya, alhali za a iya samar da shinkafar a gida Nijeriya mai tsafta da inganci, mara cutarwa.

Qalubale@gmail.com

Yakamata gwamnati ta rufe hanyar jirgin kasa ta Abuja-Kaduna

Gamammiyar kungiyar cigaban al’umma a Najeriya mai suna Coalition of Civil Society Organisations sunyi wata zanga-zanga ta lumana ranar Juma’a 13/9/2019 a Kaduna.

Kungiyar tayi kira ga Gwamnatin tarayya tayi gaggawar rufe hanyar zirga-zirga tsakanin Abuja-Kaduna a jirgin kasa, wannan ya biyo bayan yadda masu garkuwa da mutane suka maida hanyar mota Abuja-Kaduna wajen cin karansu ba babbaka.

Kungiyar tace duk wani mai fada a ji daga kan manyan ma’aikata zuwa manyan yan kasuwa da manyan ‘yan siyasa da manyan sojoji sun koma tafiya a jirgin kasa domin gudun haduwa da ‘yan garkuwa da mutane.

Jirgin kasa kuma anyishi domin talakawa su amfana amma yanzu ya gagari talaka, gashi kuma yayi tsada, masu kudi sun saye tikiti sun bar talakawa dole subi hanyar mota da ‘yan garkuwa ke sintiri, inda suke rasa rayukansu yayin da akayi garkuwa dasu saboda basu da kudin da zasu iya fansar kansu.

Kungiyar tace ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta rufe hanyar jirgin kasa domin manyan jami’an gwamnati su dinga bin hanyar mota saboda suna tafiya da jami’an tsaro da jerin gwanon motoci wanda yin hakan yana rage sintirin ‘yan garkuwa da mutane akan wannan titin inji daya daga masu zanga-zangar Yusuf Amoke.

Qalubale@gmail.com

AIKIN GWAMNATI DA ALBASHIN MA’AIKATA A NAJERIYA

Matasa, bayan sun kammala karatu basu da wani buri sai samun dacewa da aikin gwamnati a matsayin sakamako karatun nasu.

Shi aikin gwamnati idan muka duba, ana shafe shekaru 35 ana yinsa matukar babu wata matsala, sai dai kuma idan ya yi shekaru 60 da haihuwa, anan shima dole ma’aikacin ya ajiye aikin nasa.

Idan muka duba, shi ma’aikacin gwamnati yana shafe dukan rayuwarsa a bakin aiki, domin kuwa idan muka lissafa lokacin da ma’aikacin ya fara aiki misali yana shekaru 25 kuma ya kammala aikin bayan shekaru 35, idan mun hada shekarunsa na haihuwa zai kama 60 kenan daidai.

Shekaru 60 a duniya ba karamin abu bane, domin a lokacin babu abinda mutum ke nema a duniya sai hutu sai salatin Annabi da hailala da istigfari, ma’ana shekaru sun shude an tafi gangara sai neman daidaitawa tsakaninsa da ubangijinsa, a wannan lokaci kuma zaka dinga neman yadda zaka sami kulawar gwamnati domin ta biyaka hakkin da ya rage naka a hannunta, bayan duk kagama salwantar da rayuwar ka wajen bautawa jama’a.

Wasu mutane basu dauki aikin gwamnati aikin bautawa jama’a bane, sai lokacin da ma’aikata suka shiga takun saka da gwamnati wajen neman gwamnatin ta kara musu albashi ko alawus na aiki, anan jama’a suke gane amfanin ma’aikata a garesu, idan sunje asibiti ba likita ko a makarantu ba malamai ko abin Allah ya kiyaye ana gobara, babu ma’aikatan kashe gobara ko a gidan ruwa babu masu bude ruwan sha, dadai sauransu.

Shi kuma albashin na ma’aikata, bai taka kara ya karya ba, dayawa daga jama’a idan kace suzo ga aikin gwamnati kuma ga albashin da za’a biyasu bayan kowane wata, ba zasuyi ba, saboda albashin babu abinda zai yi musu wajen gudanar da kansu da iyalinsu, wannan albashin shine fa gwamnatocin Najeriya suke kyashin biyan ma’aikatan.

Babu wani ma’aikaci da yake jin dadin albashinsa a Najeriya saidai kawai idan yana wani bangare da kudin gwamnati ke wucewa ta gabansa, kuma baya iya kauda kansa sai ya taba, yin haka kuma haramun ne, idan ya mutu Allah zai tambayeshi, haka kuma a duniya, zai hadu da danasani yayin da yabar aiki, saboda samun irin wadannan haramtattun kudade ya kare, gashi kuma ya saba da rayuwar kece raini shi da iyalansa, shikenan kuma an shiga wani hali.

Don haka, idan muka duba, duba irin na hankali, zamu gane cewa babu wani dadi a aikin gwamnati tun daga farkonsa har karshensa sai asarar rayuwa da kayi kana aiki ba tare da ka amfani irin basirar da Allah ya hore maka ba, ta hanyar bujuro da wasu sana’oi wadanda zasu amfaneka tare da iyalinka da kuma sauran al’ummah, yakamata matasa suyi karatun tanutsu, su gane cewa aikin gwamnati shine abu na karshe da zasuyi bayan duk wata dama ta gushe daga garesu.

Kada matashi yana da kuruciya ga kaifin basira ga karfin jiki, ya batawa kansa lokaci wajen neman aikin gwamnati, saboda gwamnati zatayi ta yaudararsa wajen samar masa da albashin da zai iya taimakon kansa da iyalinsa ba tare da sun cika alkawarinsu ba, haka kuma bayan ya gama aiki ta hanashi hakkokinsa da zai amfana dasu koda wajen yin wata karamar sana’a ne, daga karshe haka zai hakura a bisa dole har wani lokaci ma ta Allah ta kasance, babu wanda zai kalli iyalinsa da yabari a raye.

Wannan shine qalubalen rayuwar aikin gwamnati da albashin ma’aikata a Najeriya.

Na’Allah Raheemeeb

Qalubale@gmail.com

7/9/2019

Sayarda hasken lantarki ko sayarda duhu?

Hukumar bada hasken lantarki a Najeriya wacce duk wani dan Najeriya ke tunanin samun gamsashshan hasken lantarki daga gareta domin gudanar da harkokin yau da kullun sun gaza.

A Najeriya yanzu haka muna shafe awanni 21 daga cikin awanni 24 babu hasken lantarki, ma’ana muna iya samun hasken lantarkin ne na awanni 3 kacal a kowace rana, kai wata ranar ma gaba daya haka zamu kwana mu wuni batare da ganin hasken lantarki ba.

Wannan hukumar bada hasken lantarki tayi sanadiyar durkushewar tattalin arziki da masana’antu kanana da manya da asarar rayuka sakamakon cututtuka barkatai, sanadiyar rashin hasken lantarki.

Dukkanin hanyoyin da Gwamnati yakamata tabi domin dawo da darajar samar da hasken lantarki yakamata tabi, babu wata kasa a duniya da aka sami cigaba a cikin duhun dukununu, kananan kasashen Afirika tuni suka wuce sa’anninsu harma da yayyansu a harkar baiwa al’ummarsu hasken lantarki, wasu ma har yayi musu yawa bazasu iya shanye abinda suka mallaka na hasken lantarkin ba.

Wadanda Gwamnati ta mallakawa alhakin samar da hasken lantarkin ga al’umma sun gaza, aikin su kawai sayarwa da mutane “duhu” maimakon “haske” duk watan duniya zakaga suna zagayawa da takardun biyan kudi, inda duk wata sai kudin ya hau fiye da na watan baya.

Yaya za’ayi a gidajen talakawa masu amfani da kwan lantarki uku ko hudu a kowace rana, amma karshen wata a kawo musu takardar biyan kudi Naira dubu goma ko fiye da haka?

Muna kira ga Gwamnati suyi gaggawar chanja wata hukumar wacce zata iya gudanar da wannan aiki, Gwamnatin tayiwa al’umma alkawarin kawo chanji da cigaban rayuwarsu shine dalilin zaben da suka fito suka gudanar, ba zabe sukayi domin zama cikin duhun dukununu ba.

Qalubale@gmail.com

Dan daudu Bobrisky

Yanzu haka a Jihar Lagas ta Najeriya ‘yan sanda sunkai farmaki wajen gudanar da bukukuwan cika shekaru 28 na wani fitaccan dan daudu mai suna Idris Okuneye, wanda kuma akafi sani da Bobrisky.

Shidai wannan dan daudu ya shahara wajen siffanta kansa da mata inda kana ganinsa zaka rantse cewa mace ce, ya shirya gudanar da wannan bikin zagayowar ranar haihuwar tasa ne a yau Asabar 31/8/2019 a wani dandalin shakatawa a Legas, nan take ‘yan sanda suka kai sumame kuma suka damke wasu abokan hulda da shi Bobrisky.

Amma shi gogan naka ya tsallake rijiya da baya saboda basu sameshi a daidai ba, ‘yan sandan sunce ko kusa bazasu bari aci gaba da gudanar da irin wannan masha’a ba, domin ya sabawa dokar kasa, don haka sun baza jami’ansu a duk guraran da wannan dan daudu tare da abokan huldarsa suka shirya yin liyafar tunawa da ranar haihuwar tasa.

Allah yai mana tsari da wulakanta halittar da ya tsara mana, kuma yasa mufi karfin zuciyarmu, ya kare zuriyar mu baki daya.

Qalubale@gmail.com

SADAKATUL JARIYA

Assalamu Alaikum

Kayi kokari ka sayi gida domin karantar da musulunci ga yaranmu tun daga matakin nursery, primary, da kuma higher Islamic; akan kudi naira N1,000 kacal.

Mu musulman Rivers state karkashin (JIBWIS 1) muna son mu sayi gida a no 19 Echiwe street, mile 2 Diob, Portharcourt, domin karantar da Islamic studies, hakan ya faru ne saboda rashin muhallin kanmu da kuma tsadar biyan kudin haya kowane shekara.

Shi yasa Muke neman taimakonka/ki domin sayen wannan gida a mastayin *SADAKATUL JARIYA* a gareka/ki.

Idan da za a samu mutane 30,000 kowanne daga cikinsu ya bada N1,000 zamu samu Miliyan (30m)
Kuma Dama kudin gidan kenan miliyan 30 (30m).

Duk abinda kabayar wajan wannan taimakon; muna ronkon Allah (SWT) da Ya rubanya maka ninkin baninki.

Zaka iya bada naka taimakon ta wannan account:
NAME: JIBWIS RIVERS STATE PROJECT
ACCT. NO: 3136508699
BANK: FIRST BANK

RSVP:
Ustaz Ahmed Ishaq 08035578206

Ustaz Muhammed Jibril
LK 08037596056

Alh. Sunusi Adamu 07061684482

Imam Sulaiman 08069059015

Alh Muhd Ali Kwade 08033101224

Abdullahi Ya’u 08039737287

Domin girman Allah (SWT) ka/ki taimawa addinin musulunci ka/ki turawa mutane da kuma group group

#Qalubale@gmail.com

SABON TSARIN DUNIYA (NEW WORLD ORDER) -KASHI NA FARKO (1)

Daga Datti Assalafiy:

Tsari ne da duniyar yau take bisa kai, wanda wadanda suka tsara wannan lamari, sune masu Bautar Shaidan tare da taimakon Yahudawa. Duk wata harkar cigaba na Duniya a a yau sune kan gaba, kuma sunfi kowa qwarewa akai, indai abunda ya shafi Duniya ne. Shiyasa Allah madaukakin sarki, yake ce mana:

{يَعْلَمُونَ ظَاهِرًا مِّنَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَهُمْ عَنِ الْآخِرَةِ هُمْ غَافِلُونَ} [الروم:7]

“Sun san Zahirin rayuwar Duniya (Sun qware sosai). Amma game da Lakhira ranar Gobe Qiyama, su Gafalallu ne (Jahilai)”

Kaga ashe su ba jahilai bane, don Allah Ya basu ilimin sarrafa abubuwa a Duniyan ce, harkar Siyasa sune kan gaba, harkar tattalin arziqi babu wanda ya kai su. Tsabar su nsan Duniya, shiyasa cikin Tafisrin Ibnu Kathir a qarqashin wannar Ayar da ta gabaga, yake cewa, Hasanul Basry (Rahimahullah), Yace:

قال الحسن البصري رحمه الله: “والله ليبلغ من علم أحدكم بدنياه، أنه يقلب الدرهم على ظفره فيخبرك بوزنه، وما يُحسن أن يصلي

“Wallahi, ilimin dayan ku game da Duniyar sa, akai matsayin da zai dinga juya Dirhami (Kudi), akan kimantawar sa, ya kuma bada labari nauyin sa (Adadin sa), amma kuma zaka samu baya Sallah balle ya kyautata ta”

A cikin Tafsirin Qurdabiy, shima a qarqashin wannar Ayah ya kawo maganar Ibnu Khalawaihi, da cewa:

وقال ابن خالويه: “ما كان أعرفهم بسياسة دنياهم”

“Babu wani da ya kasance a Duniya wanda ya fisu sanin Siyasar Duniyar”

Ko shakka babu, sun samu nasara kashi Talatin ko Arba’in cikin Dari kan abun da suke nema. Basu fasa ba, suna nan suna kai. Duk wata hanyar sadarwa nasu ne, suna da kaso mai tsoka ciki, sannan ta 6angaren sadarwa sun samu nasara gagarumi.

Babbar manufar su shine, bautar Shaidan zata cika Duniya, hakan shine babban mafarkin su na mallakar Duniya. Tsari ne da suka jima suna yi. Burin su ba wai sai kaje kana bauta wa Shaudan ba, ah ah, su dai su raba ka da Allah ta hanyar cusa maka wani tunani, da wasu abubuwa na jan hankalin al’ummah, karshe kai da kan ka, zaka ji kana qyamar addinin ka, sai ka dinga ganin hakan a matsayin Kauyanci ne.

Duk wata kafar sadarwa (Media), suna da kaso mai yawa a ciki, babu wani labari da za’a sake wa Duniya face suna da iko akai, sai abun da suka so ake bayyanawa. Tun daga kan Facebook, Instergram, Tweeter, WhatsApp, da saura su, suna daga cikin sabbin hanyoyin su na ganin dukkan abubuwa dake faruwa a fadin Duniya baki daya.

Babu wani shugaba daga cikin shugabannin Duniya, face dolen sa yana musu biyayyah kan wasu qudurorin su, har kasashen Musulmai, Ina nufin duk wata Kasa mai suna Kasa (Country) a Duniya, kuma duk wani shugaba mai suna shugaba a Duniya. Idan kaga shugaba yana nuna kishin sa kan addinin sa, musamman Musulunci, ba wai a son ransu yake hakan ba. Idan suka samu dama zasu saka shi a gaba da makirici kala kala.

A duk cikin addinai da ake dasu a fadin Duniya, Musulunci shine addinin da suke shakka, duk da cewa, daga cikin musulmai akwai wakilan su da sunan musulunci, kamar Yan Boko Aqeedah, da wash Aqeedu gur6atattu, duk wakilan su ne dake taimaka musu wajen ganin sun cimma manufar su.

Idan aka zo batun shirin fina finai (Film/Movies), duk wakilan su ne, ko sun sani ko basu sani ba. Shiyasa suke anfani da kalmar “Wood” Ma’ana waje inda bishiyiyi da tsiranni ta mamaye. Daman burin su shine, su mamaye Duniya, na kowani kasa akwai taken sa. Bollywood, Hollywood, Kannywood, da sauran wood wood dake tashe a Duniya, ko ake anfani domin shirya fina finai.

Daga cikin mafi munin fina finai shine, Pornography Films, abunda galibin mutane suka fi sanin sa da “Blue Film” (shudin fim, ko fina finan batsa) sune manya manyan jakadun su a Duniya. Wannan 6angare, yayi matuqar taka rawan gani a Duniyar Matasa wajen lalata rayuwar su, har da masu qoqarin riqo da addini daga cikin matasa, sai wanda Allah ya tseratar dashi da tserewar Za. Zai yi wuya ka samu Matasa Goma maza ko mata, ba tare da ka samu Pornography films da videos na Blue films ba wayoyin su na sadarwa (Phone).

Babban burin su na samar da ire iren wadannan fina finai shine, sun san babu wani abu mai qarfi wajen jan hankalin dan Adam irin sha’awa, matukar idon mutum zai kai ga ganin al’aurar mace. Matuqar mutum zai ci yasha dole sai sha’awa tazo masa, tunda Dabi’ce da Allah madaukakin Sarki ya dabi’antar da bayin Sa kai, musamman idan mutum yakai munzalin Balagha. Shiyasa idan kaga matashi (Saurayi), ko matashiya (Budurwa), yana yawa kadautuwa a daki shi kadai da wayar sa (Phone), dayan biyu ne, imma yana karatu dashi wanda ya kunshi harkar duniya, ko na addinin sa, imma ka samu yana kallon fina finai na batsa (Blue film). Allah kadai yasan irin dumbin yawa matasa da suke kallon wadannan fina fina na batsa a Duniyar mu ta yau. Sai wanda Allah Ya tsare.

Babban masifa da fitintinu da kallon ire iren wannan fina finai ya haddasa tsakanin Samari da ‘Yan mata (Matasa) shine, afkawa Zina ciki Sauqi. Yarinya budurwa zata iya zuwa waje saurayin ta ko shi yazo ya same ta, suyi duk abunda suka ga dama ba tare da iyayen ta sun san ta aikata wani abu a waje ba. Shiyasa hatta Karuwai sun fahimci kasuwar su ta ja baya. Abun bai tsaya nan ba, har da matan aure, mace zata iya fita waje, taje tayi lalata da wani duk da cewa tana da aure. Sannan, akan samu magidanci ya fita ya bar iyalin sa, shima yaje yana lalata da matar da ba tashi ba.

Abun bai tsaya nan ba, ya janyo mata dayawa, Budurwaye da mata aure sun fada cikin aikata Madigo (Lesbianism) tsakanin su. Ni jiyau ne, domin na saurari koke dayawa daga wajen ‘yan mata wadansa sunyi nisa sosai cikin harkar, suna so su daina sun gagara dainawa, sai suke neman hanya da mafita da zasu bi don su daina. Haka nan, masu Luwadi (Homosexual), tsakanin maza da maza, namiji yana neman dan’uwan sa namiji, domin biyan buqatar sa, suma harda magidan ta masu aure, duk sun afka cikin haka. Shima jiyau ne waje na, domin ansha samu na da maganar domin samun mafita, hanyar da za’a ayi a daina.

Mafi qarancin abunda kallon wadannan fina finai suka janyo tsakanin al’ummar matasa, musamman marasa aure, daga mazan har mata, duk da cewa shima babbar fitana ce, amma bai kai na baya da na ambata ba. Daga cikin abunda ya haddasa wa matasa shine, yawan “MASTURBATION” da harshen larabci muna ce masa ‘ISTIMNA’I” shine mutum ya dinga shafa gaban sa yayin da yake kallon irin wannan film na batsa. Maza da mata dayawa idan suka kadaitu zaka samu suna aikata haka cikin dakunan su na kwana. Namiji yana shafa gaban sa, ita ko mace tana shafa gaban ta da sanya yatsun ga cikin gaban nata, har mutum ya samu yayi Inzali (Release). Daga cikin fitinar, sun qirqiro hanya mafi sauqi na abunda zasu dinga anfani dashi wajen aikata haka.

Daga cikin hanyoyin da suka qirqiro shine, wani abu da ake cewa “DILDO VIBRATOR” Anyi shi ne yanda siffar gaban namiji yake (Al’aura), yana da matuqar laushi da taushi, wanda duk wacce ta sanya a gaban ta dolen ta ta samun biyan buqata. Ba kowanne bane vibrator, akwai wacce mace ita da kanta zata dinga sanya shi cikin gaban ta tana cirewa tamkar yanda ake jima’i. Haka nan ma, sun qirqiro na maza, sun sawwara shi tamar gaban mace, shima yana da laushi da taushi sosai, yanda daga Namji ya sanya gaban sa ciki shikenan ya gama samun dadi da yake nema. Duk wadannan abubuwa kadan ne daga cikin shirye shiryen su na mallakar Duniya domin bautar Shaidan.

Dayawa daga cikin yaran masu hali musamman ‘yan mata, wasu daga ciki suna dashi suna anfani dashi, abin takaici harda matan aure, sai wacce Allah Ya tsare. Shiyasa aure musamman a zamanin da muke ciki yanzu baya daurewa, domin galibi daga Mazan har matan an sanya Sha’awa da karya, wanda shima zanzo nayi magana akan su nan gaba, duk yana daga cikin shirin su na mallakar Duniya. Wadannan mutane duk yanda kuke tsammanin su indai game da Duniya ne wallahi sun fimu sanin komai akan ta da hanyoyin da zasu hallaka mutane, daman Shaidan suke bautawa “ILLUMINATI” ko kace “FREEMASON” duk tafiyar su daya.

Ku gafarce ni, zan tsaya anan. Sai a rubutu na gaba zan fito da wasu bayana nan filla filla. Abun zan fitar na nan gaba wanda duk yana daga cikin makirce makircen su na hallaka Duniya ta koma bautan Shaidan, sune kamar haka:

1. ILLOLIN WAYA (PHONE),
2. CELEBRITIES (MUSICIANS, ACTORS, AND FOOTBALLERS)
3. MATSALOLIN DA SUKA QUNSHI MATASA DA MA’UARATA WANDA DUK DALILIN MAKIRCE MAKIRCEN SU NE.

Signed: Motivator & Author Barr. Kalimullah Ahmad Hinna

Allah Ya tsaremu daga sharrin yahudu da nasara.

#Qalubale@gmail.com

Ku kiyaye mu’amala da mazambata a yanar gizo

Daga Bello Iliyasu Hussain

Don Allah wanda yasan Kauthar Muh’d Kabir Ya gayamata kodai wani yayi hacking din account dinta ko kuma tana backing wrong horse.

Jiya anyi min inbox daga account din kauthar cewa tana Amerika zata dawo najeriya ranar Lahadi zata sauka a Legas saboda haka in taimaka in bawa Direbanta Naira dubu 8 yasa Mai ya dauko ta a iyafot. Ta turo min da bayanan banki kamar haka:-

K Kabir
0041006127
Union Bank

Can kuma bayan nace ba network, sai tace/yace in bayar da Number wayata zata bawa direban da safe ya nemeni. Take na bata number ina jiran inga mara kunyar direban da zai kirani.

Ilai kuwa ina tashi daga bacci sai ga six missed calls daga direbobin Kauthar da wannan nambobin:-
08033193388
08031561116

Ashe direbobin har biyu aka turo min. Daya daga ciki ya turo min bayanan Banki kamar kamar haka:-

Mustafa Ismail
GTB
0111076030

Dayan kuma yace min zaizo Zoo Road ya karbi Kassshhh baya son transfa.
Kajifa! tun daga legas zaizo Kano ya karbi dubu 8 ya koma legas yaje iyafot ya dauko hajiya Kauthar.

Yanzu dai mun hada duk bayanan da muke nema akan kauthar da direbobinta, kuma zamu miqashi inda ya dace. Idan ma ta fasa dawowa najeriyan to a amerikan ma munsan yanda zamuyi da ita tunda F.B.I ma suna list dinsu

Masu mu’amala da ita kuma sai su kiyaye!

#Qalubale@gmail.com

WANNAN AI ABIN KUNYA NE!

Daga Umar Faruq Muhammad:

Jiya nake ganin Labarin wani zama da Gwamnatin Tarayya zatayi a watan Satumba don tattaunawa da ‘Yan Kwadago akan karancin Albashi, tattaunawa ta nawa?

Idan Ma’aikatar Labour zatayi amfani da ta Ido tayaya zata kalli Yan Kwadago bayan a baya sun cimma matsaya?

Yanzu don Allah da wanne irin Idanu Gwamnatin Tarayya zata kalli Talakawan kasa musamman Ma’aikata?

Kun samu ‘Minimum wage’ #18,000, a lokacin Buhun Shinkafa #7500, Litar Mai #97, sauran kayan Masarufi da sassaukan farashi.

A lokacin wannan Gwamnatin Shinkafa sai da ta kai #20,000, yanzu tana #14,000+, Gwamnatin da kanta ta maida litar fetur #145 maimakon #97 da ta tarar dashi, yanzu don Allah kuna ganin kun kyautatawa masu ‘minimum wage’ na #18,000 din can?

Magana ta Gaskiya babu alamar Rahama a wannan Matakin, babu wani yanayi dake nuna tausayin talaka cikin wannan tsarin.

A gani na da ku dauki tsarin yaudarar Ma’aikata akan karin Albashi gwara kuce KUN GAZA BAZAKU IYA BA!

Gaskiya nafada muku, in kun dauka kanku, in baku dauka ba mu kuka jawowa abin fada!

#Qalubale@gmail.com

Allah Gwani | Abubuwan ban mamaki goma dangane da zuciya.

Daga Shafin Physio Hausa

1] Zuciya tana fara bugawa tun kwanaki 22—23 da halittar ɗan-tayi a mahaifa.

2] Girman zuciyar mutum ya kai girman dunƙulallen hannun mutum.

3] Zuciya tana bugawa sau 60—100 a minti ɗaya yayin hutu — yayin da ba’a aiki.

4] Zuciya tana bugawa kimanin sau dubu ɗari (100,000) a kowacce rana.

5] Zuciya tana buga ko harba jini da ya kai yawan galan dubu biyu a kowacce rana.

6] Zuciya tana iya cigaba da bugawa bayan an cire ta daga jiki.

7] Zuciya ta dogara ne da tsarin lantarki domin bugawa.

8] Jarirai na da bugun zuciya mafi sauri da ya kai bugu 70 —190 a minti ɗaya.

9] Zuciya tana harba jini zuwa jijiyoyin jinin da tsayinsu ya kai mil dubu sittin (60,000 Miles) in da za’a warware su.

10] An fara yin tiyatar zuciya a shekarar 1893, wanda likitan zuciya Daniel Hale Williams baƙar fata ɗan ƙasar Amurka ya gudanar.

#Qalubale

MEYASA FREEDOM RADIO SUKA HANA DAN BILKI PROGRAM A TASHAR SU?

Daga Umar Faruq Muhammad:

Amsar itace yayi program yasoki Mai martaba Sanusi na biyu.

Nayi wannan tambayar ne ganin yadda Freedom din sukayi wani shiri dasuke nuna cewa Gwamnatin Kano zata kama wasu mawaka saboda sabanin siyasa.

Freedom sun hana Dan Bilki magana a gidan su saboda yataba kimar Sarki, shin Sarkin Birnin Kano kadai ake cin zarafi a tashar su?

Meyasa suka bari ana taba Shaksiyyar wasu alhalin sun hana a taba ta Sarki?

Shin idan labarin kama mawakan Gaskiya ne menene bambancin aikin Freedom dana hukumar tace fina-finai? Kun hana wani kun kyale wasu, Censor ta kyale wani kunce zata kama wasu!

#Qalubale

Muna samun hasken lantarki awa 24 idan Buhari yazo

Al’umma a garin Daura ta Jihar Katsina sun shaidawa Shugaba Buhari dan asalin garin cewa, suna more hasken wutar lantarki awa 24 ne kawai idan yazo garin.

Me zaku ce game da wannan batu?

#Qalubale

SIRRIN HARAMTACCIYAR KUNGIYAR SHI’AH (IMN)

Daga Malam Datti Assalafiy:

Yau Datti Assalafiy ya cika alkawarin da ya dauka na fitar muku da wasu sirruka da ya shafi kungiyar Zakzaky

Mutane suna mamaki kuma suna tambaya akan hanyoyin da Zakzaky ya bi ya tara dunbin matasa a cikin kungiyarsa, da kuma hanyar da yake samun kudaden da yake amfani da su wajen gudanar da harkokin kungiyarsa alhali baya kasuwanci, kuma baya aikin gwamnati, da kuma abinda yake rinjayar matasa shiga cikin kungiyar

Nigeria kasa ce da Allah Ya albarkaceta da yawan musulmi, kuma ana son musuluncin da gaske, Zakzaky yayi amfani da damar soyayyar da ake yiwa Musulunci ya fara kira akan a bishi zai jagoranci kafa gwamnatin shi’ah a Nigeria da yake cewa wai gwamnatin musulunci

Sannan Zakzaky yayi amfani da halin kunci na sha’awa da son jima’i wanda yake addabar matasa, gashi ba su da halin yin aure, sai ya halasta musu zina ya fakaice da mut’ah, kwadayin son jima’i ya jefa dubbannin matasa maza da mata cikin kungiyar Zakzaky

Jama’a bakwa mamaki abinda yake faruwa a Abuja? ‘yan mata ne musulmai manyan ‘ya’yan attajirai suna killace a gida, sunyi karatu sun gama jami’ah suna son aure amma babu mazajen da zasu aure su, da yawansu sun fada kungiyar shi’ah domin su dinga rage sha’awar da take addabar su, ‘yan mata da yawa suna cikin kungiyar ba tare da sanin iyayensu ba ana lalata da su

Amma duk da wannan jama’a da ya tara, Zakzaky ya san cewa ba zai samu nasaran kafa gwamnatin shi’ah ba face sai ya samu goyon baya daga gurin manyan ‘yan siyasa da manyan jami’an tsaro wanda zasu taimaka masa wajen hambarar da gwamnati da karfin tsiya, kamar yadda magabacinsa yayi a Kasar Iran, shiyasa sai ya jira har zuwa ranar da ‘yan kungiyarsa suka haye madafun iko kafin sai ya wanzar da kudurin nasa

Zakzaky yana da hanyoyin samun kudi guda biyu, na farko tallafin kudi da Kasar Iran take bashi, na biyu kudin zinar mut’ah da mutanensa talakawa, manyan ‘yan boko da attajirai suke biya, bincikenmu ya tabbatar mana da cewa duk wanda zai biya kudin mut’ah ba za’a bawa budurwa ko matar da za’ayi mut’ah da ita kudin ba, kudin na Malam ne, ko da za’a bata amma dai Malam shi ke da kaso mai yawa, shi ake tarawa kudin, akwai masu yin zinar mut’ah na kwana biyu, sati daya, wata daya da sauransu, ko kwana nawane mai son auren mut’ah ya zaba da farashinsa, har ana iya samun juna biyu

Shekarun baya, na taba fada muku wani labari da ya faru, wata ‘yar shi’ah ce ta rinjaye kawarta ta shigar da ita harkan mut’ah aka dirka mata cikin shege, rana tsaka uban yarinyar suka ga ‘yarsu da cikin shege, a lokacin an dauki lokaci mai tsawo ana buga Shari’a a gaban alkali, nayi kira ga jama’a nace kowa ya saka ido akan ‘ya’yansa mata, a yanke dukkan wata alaka dake tsakaninsu da ‘yan shi’ah

Bayan wannan, lokacin da Zakzaky ya kwace ikon unguwar Gyallesu daga hannun gwamnatin Nigeria, ya sa ana yin garkuwa da ‘ya’yan mutane ana kaisu can ana horar da su ayyukan ta’addanci da aikin soji da na ‘yan sanda, yana da jami’an tsaronsa, ya nada kansa shugaban kasa, yana da gwamoninsa da chiyamomi da kansiloli, yana da jami’an tsaronsa na sirri da na fili da ‘yan leken asiri, yana da likitoci da ‘yan jaridu, har da sarakunansa na gargajiya, wasu ana horar da su anan gyalle su wasu ana kaisu Kasar Iran su samu horo na musamman

Tattaki: jama’a kun san manufar da ta sa Zakzaky ya wajabta wa mutanenshi yin tattaki a duk inda suke a Nigeria su tafi Zaria da kafafunsu? wannan wani salo ne na horon aikin soji yake musu a fakaice, haka zasu fito mazansu da matansu suna tafiya a kafa suna yada zango a makarantun firamare da sakandare na gwamnati, ance mana duk kauyen da suka yada zango idan akwai kororon roba (Condom) sai ya kare a garin, tunda sun saba da tafiya a kasa, to akwai ranar da zai umarcesu su nufi Abuja da kafa suje su hambarar da gwamnatin Nigeria ya dale kujerar shugaban kasa

Idan kuna son ku fahimci wannan bayanin, ku karanta abinda ‘dan jaridar IMN Bilya Hamza Dass ya wallafa kamar haka:
“..wannan waki’a ta yaye mana wani labulen da ya boye mana Abuja a da. Yanzu mun fahimci tituna da lungunan Abuja tun kafin shiga Abuja na sosai ya zo. Yanzu Abuja ga ‘yan’uwa kamar jariri ne da hantsar uwarsa. Kamar Maigida ne da gidansa.
Mun san Abuja kamar yadda muka san yawan kudaden da muka ajiye a aljifanmu. Mun fahimci lungu da sako-sakon garin. Babu inda kaza za ta bacewa muzuru in lokacin kalaci ya yi…” wato yana magana ne a fakaice cewa yanzu sun san sirrin Abuja, sun san hanyar fadar shugaban Kasa, rana tana tafe, ranar da Zakzaky zai umarcesu su tafi Abuja su kifar da gwamnatin Nigeria

Lokacin da suke zanga -zanga a Abuja da Kaduna, ku duba ku ga yadda suke kalubalantar jami’an tsaron gwamnati, ‘dan shi’ah zai cire rigarshi ya zo gaban soja ko police wanda yake rike da bindiga yace harba, yawancin matasan shi’ah da suke yin haka ba a hayyacinsu suke ba, wato akwai wani ruwa da akayi packaging dinsa a cikin leda kamar ledar pure watar, ana fada musu cewa wai ruwan addu’ah ce da mujahidai suke sha, alhali karya ne, binciken mu ya gano mana cewa wannan ruwan addu’ah da ake bawa sojojin shi’ah magoya bayan Zakzaky hadadden miyagun kwayoyi ne masu gusar da hankali irin wanda ‘yan ta’adda suke sha kafin su kaddamar da harin kunar bakin wake

Zaku ga a duk lokacin da matasan shi’ah suka fito zanga-zanga bayan an basu wannan ruwan sunsha suna jin wani irin karfi a jikinsu kamar kasa ba zata dauke su ba, ji suke a mutu ko ayi rai, lamari ne na miyagun kwayoyi da aka basu suka sha ya gusar musu da hankali

Duk abinda Zakzaky yake yi karshenta dai so yake yayi amfani da wadannan matasa ya kifar da gwamnatin Nigeria, amma kamar yadda na fada muku ‘yan shi’ah basa kaunar a tona musu asiri akan miyagun akidunsu da kuma boyayyun ajandarsu, kamar yadda kungiyoyin asiri masu shan jini (secret cult) da manyan kungiyoyin bayar da agaji wanda ba na gwamnati ba (International NGOs) masu taimakon kungiyoyin ta’addanci a boye, suka ki jinin a fitar da sirrin ayyukansu, to haka ‘yan shi’ah magoya bayan Zakzaky suke

Duk wani mai kaunar zaman lafiyar Nigeria da ya san sirrin manufar kungiyar Zakzaky ba zai kaunaci mutuminnan ba balle ya tausaya masa, mutane suna fadin cewa me yasa gwamnatin Nigeria take takura masa? amsar shine yana cin amanarta, yana so ya kafa kasa a cikin kasa, Shehu Dahiru Usman Bauchi yafi Zakzaky yawan mabiya, me yasa gwamnati bata takura masa ba? amsar shine baici amanar gwamnatin Nigeria ba yana son zaman lafiya, Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau yafi Zakzaky mabiya, amma me yasa gwamnati bata takura masa ba? amsa shine baici amanar gwamnatin Nigeria ba

Yau inda ace Zakzaky zai nada kansa a matsayin Allah abin bauta, ya umarci mutanensa akan cewa su bauta masa, matukar bai taka dokar kasa ba ya zauna lafiya, babu ruwan gwamnatin Nigeria da abinda yakeyi, gwamnatin Nigeria zata bashi cikakken tsaro da kariya a matsayinsa na ‘dan kansa

Allah Ka tsare mana Kasarmu Nigeria daga sharrin kungiyar Zakzaky

#Qalubale

YADDA SOJA SUKA KASHE ‘YAN SANDA A TARABA

Daga Muhammad Bello Sharada:

‘YAN sandan Najeriya sun dauki tsawon lokaci da dade wa suna kokarin cafke Alhaji Hamisu Wadume. Bincikensu ya tabbatar hamshakin dan garkuwa da mutane ne, ya yi kaurin suna a Jihar Taraba. Kwanan nan ma Alhaji Hamisu ya karbi kudin fansa naira miliyan 100 da suka karba a hannun wani da suka yi garkuwa da shi.

A sakamakon haka, aka yi shiri na musamman aka tashi tawagar Intelligence Response Team IRT wacce sufeto janar na ‘yan sanda ya kafa. Wannan sumamen an yi shi a karkashin ASP Felix Alodije.

Cikin nasara ‘yan sanda suka kamo Alhaji Hamisu Bala Wadume suka saka masa ankwa suka taho da shi. A lokacin da zasu gudanar da wannan aikin sun hada da karin ‘yan sanda a hedikwatar ‘yan sanda da ke Jalingo.

Tsautsayi, akan hanyarsu daga Ibbi zuwa Jalingo suka hadu da sojoji.

A bayanin da rundunar sojoji ta yi, ta ce waya aka yi wa su sojoji cewa ga wasu masu garkuwa sun sace Alhaji Hamisu Bala Wadume. Kuma mutanen da suka yi satar suna cikin mota Hiace mai lamba LAG MUS 564. Sojojin runduna ta 93 da ke Takum a wurin chekin guda uku sun nemi wadannan mutanen su tsaya suka ki, dole suka bi su da gudu bayan sun bude musu wuta suka rika dauki ba dadi da su. Daga karshe a sanadiyyar haka suka kashe ‘yan sanda uku da civilian daya kuma mutum hudu sun ji munanan raunuka.

Sai bayan da aka yi wannan ba- ta – kashin ne, sojoji suka gano ai ‘yan sanda ne suka zo yin aiki cikin sirri, wanda basu da masaniya akansa, kuma sun yi tambaya babu bayani, hakan har ya kai ga mutuwar wasu kwararrun aikin yan sanda da suke tare da IRT.

Amma kuma jami’an ‘yan sanda, sun ce sojoji fa karya suka tsara don haka suna da tambayoyi guda shida ga sojoji. Suna son a fada musu wanene ya yi wa sojoji waya? Suna son su sani ta yaya aka yi Alhaji Hamisu Bala Wadume ya samu kubuta? Yanzu Alhaji Hamisu Bala Wadume yana ina? Da sojoji suka kama Alhaji Hamisu Bala Wadume sun tsere shi kuma sun dauki bayaninsa kamar yadda tsarin aiki ya tanada? Yaya aka yi soja suka rika harbin ‘yan sanda alhali gasu a gabansu kuma wasu cikin yan sandan sun gaya musu aiki suka zo?

Abin takaici wadannan ‘yan sanda da aka kashe suna cikin tawagar shahararren dan sandan nan Abba Kyari da suka samu horo na kwarewa akan harkar garkuwa da ta’addanci daga kasashen duniya. Suna cikin wanda suka kamo Evans kuma kwanan nan suka tserar da Magajin Garin Daura.

An kafa kwamitin bincike akan wannan musiba a karkashin DIG Mike Ogbizi. Zamu kasa kunne mu ji, don wannan batun bai kamata ya tafi haka a banza ba. An kashe ma’aikata na musamman, sojoji su ci gaba da harkarsu shike nan, shi kuma Alhaji Hamisu Bala Wadume ya ci banza kenan, kuma zaman lafiyar da ake son samu shima babu?

Duk wadannan bayanan na samo sune a hannun Cif Frank Mba na rundunar ‘yan sanda da Hafsan soja Sagir Musa.

KA TABA YIN ZINA?

Daga Nasiru Abubakar Gombawa:

Fitinar Sha’awa kashi na 04.
Tsaya kuji irin mummunan Bala’in da zina ke haifarwa. Zina tana cikin manyan laifuffuka, wanda dukkan shariun da Allah ta’ala ya saukar sun hadu akan haramcin zina.
Al kur’ani mai girma da Sunnar Annabi (S.A.W) da dukkan Malamai sun hadu akan haramcin zina.
Qofofin zina guda biyar ne kamar haka:
1- Kallo zuwaga Abinda Allah ya Haramta.
2- Shigar batsa
3- Kalaman Batsa
4- Kebancewa da matar daba muharrama ba
5- Sha’awa Mai karfi babu aure
Allah taala yace:
“kada ku kusanci zina”
Manzon Allah (S.A.W) yace: Mai zina ba zaiyi zina ba, yayin da yake zina, sai an cire masa imani.
Abdulllah Dan Mas’ud Ra yace: Duk Al’ummar da take zina, ta jawo wa kanta fushin Allah, da halaka.
Musulunci yayi umarni da tsare abubuwa guda shida sune kamar haka:
1-Addini.
2-Dukiya
3-Rayuka
4-Hankali
5-Mutunci
6-Nasaba
Amma zina ita kadai, tana rusa wadannan duka. Hukuncin mazinaci, mai aure kisa ta hanyar jifa. Saurayi mara aure Bulala dari da daurin shekara.
Ana tabbatar da zina ta hanya uku.
1-Shaidu guda hudu.
2-Mutun yayi ikirari da kansa.
3-Samun mace da ciki, babu aure, ko shubha.
Bisa sharudda da aka sanyawa ko wanne. Zina wata babbar musiface da bala’i da dukkan sharri, datake ruguza al’umma, take wargaza iyali, take tarwatsa gari, take rushe mutunci, take jawo karayar tattalin arziki, da fatara, da tsiya, da annoba, acikin rayuwar dai dai ku, da gidaje, da unguwanni, da gururuwa, da kasashe, da duniya baki daya.
Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake samun dukkan sharri kamar haka:
1- Raunin Addini
2- Raunin Akida
3- Karancin Imani
4- Rashin kunya
5- Rashin kishi
6- Rashin mutunci
7- Rashin kwarjini
8- Rashin hasken fuska
9- Duhun zuciya
10- Rashin kima
11- Rashin Nagarta
12- Rashin Nutsuwa
13- Rashin Amana
14- Fushin Allah
15- Cikawa babu imani
16- Azabar Allah.
Allah ya tsare mu da zuriyar mu, da dukkan
al’ummar musulmi daga afkawa bala’in zina.
Wadanda sukeyi Allah ya shiryesu.
Gabatarwa:-
Assalafy
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
* HUDUBAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WANDA YAYI A KHUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH, SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARFA KENAN).*
*ANNABI (SAW)YA FARA DACEWA:*
“`“Ya ku mutane ku bani hankalinku, domin mai Yiwuwa bazan sake kasancewa da ku bayan wannan shekaran ba, saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda basa wannan wuri a yau.
Ya ku mutane kamar yadda kuka riki wannan wata, (na hajji) da wannan rana (ta arfa) da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa, to, haka kuma ku riki Ran Musulmi da kuma Dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa, ku maida wa Mutane kayan da suka baku Amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu su cuce ku, ku tuna fa, hakika ALLAH zai yi sakayya akan ayukakanku, ALLAH (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi.
Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye Addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka ku guji binshi akan kanana.
Ya ku jamaa hakika kuna da hakki bisa matayenku, amma suma suna da hakki bisa kanku, to hakkin su ne akanku da kuciyar dasu, Kuma ku tufatar dasu akan jin kai. ku bi dasu kyakkyawan biyarwa, ku kuma tausasa musu domin su majibintan al amurran kune, kuma mataimakan ku, Hakki ne akansu da kar su yi abota da duk wanda ba kwa so, kuma su nisanci zina.
Ya ku jama’a kuyi kyakkyawan bauta ga ALLAH (SWT) ku tsaida salloli biyar(5) na farilla, Ku Azumci Watan Ramadan ku Kuma bada zakka. Ku aikata aikin hajji in har kun sami daman yi. KU SANI FA, ko wane musulmi dan uwan musulmi ne. Dukkan ku dai dai kuke. Ba wanda yake da fifiko saman wani sai ta tsoron ALLAH, da aikata kyawawan ayyukka.
Ku tuna fa(ya ku jama’a) wata rana za ku tsaya gaban ubangijinku, domin sakamakon ayyukanku, saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da hanya madaidaiciya bayan na kau.
Ya ku jama’a ba wani annabi ko manzo da zai zo bayana kuma babu wani addini da zai zo (bayan addinin musulunci), saboda haka kuyi tunani sosai akan wannan magana dana gaya maku, kuma ku fahimce ta (sosai).
Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); ga (alkur ani) ga kuma (sunnah) ta. In kun bi wannan ba za ku ta ba bata ba. Duk Wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, suma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji magana daga karshe sufi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada.
YA ALLAH ka zamo shaida agareni, cewa na isar da aikenka zuwa ga bayinka.” Yan uwa ku watsa wannan KHUDUBAR ga yan uwa musulmi wanda kamar yau akayi ta!!!
Allah duk wanda ya tura wannan khuduba ya Allah ka sadashi da annabin MuhammadMuhammad (saw) ya Allah kabiya masa dukkan bukatunsa na alkhairi“`

#Qalubale

Amaryar Sarkin Kano Sunusi II Ta Tare Shekaru Hudu Bayan Daura Aure

Daga El-Hajeej Hotoro Maje

Amaryar Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II (Wacce ita ce ta hudu) ta tare bayan Shekara hudu da daurin Aure.

An kawo Amarya Gimbiya Sa’adatu Barkindo Mustapha fadar Sarki ranar Asabar yayin da aka yi budar-Kai ranar Lahadi.

Amaryar ba ta dade da kammala jami’a ba a Landan jim kadan bayan an daura auren.

Idan za a iya tunawa Sarki Sanusi II ya auri ‘yar Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo-Musdafa, a yanayin auren da ba a yi gagarumin shagali ba gami da tara mutane ba a garin Yola, ranar 25 ga Satumbar 2015.

#Qalubale

Hajiya Aisha Bello Matawallen Maradun Awajen Wa azin Mata

Daga Real Sadiya Abubakar:

HAJIYA AYSHA BELLO MATAWALLEN MARADUN TAYI ALKAWALIN CIGABA DA ZUWA WA AZIN MATA DUK SATI WANDA AKEYI A WOMEN CENTER GUSAU

Tun bayan wasu shekaru masu yawa inji malan yace wallahi shekara takwas sharabo dasuga matar gwamna tazo wa azin mata kwatsam saiga maigirma First Lady hajiya Aisha bello matawallen maradun tazo wa azin mata tareda alkawalin duk sati zata cigaba da zuwa dayardar Allah

Hakika abun yabaiwa kowa sha awa irin yanda sunkaga maigirma hajiya Aisha Bello matawalle uwar marayu ta halarci gurin tareda alkawalin duk sati zatazo ayi da ita kuma hajiya Aisha bello tayi wa Allah godiya kasancewar yau tataso takanas tazo tatararda ana WA Aziz itama tasaurara kuma tayi jinjina ga matan dake halartar wa azin duk mako hakika munyi dacen uwa tagari

Bayan nan kamar yanda tasaba tayi halinnata tabaida kyautar kudi ga mahalarta wa azin inda sunkafitow suna sambarka suna Allah yayi albarka

Allah yasaka da alkhairi

Tareda ita akwai

Her excellency hajiya hadiza mahadi Ali gusau

Hajiya rahamu Hassan nasiha

Dasauran matan da sunka rufomata baya.

#Qalubale

Sarkin Rano ya dakatar da hakiman Kura, Garun Malam da Takai

Ranar litinin 29/7/2019 Majalisar Fadar Sarki Rano ta aikawa wasu hakimai uku (3) takardar dakatarwa bisa rashin biyayya ga Majalisar Sarkin.

Bayan ta karbi bayanan da suka bayar a rubuce na kariya a sakamakon tuhumarsu da majalisar tayi na rashin yin biyayya ga fadar ta Sarkin Rano, majalisar bata gamsu da amsar da suka bayar ba.

Sakamakon haka, majalisar Sarki Rano, ta yanke shawarar dakatar da hakiman kamar haka;

1) Hakimin Kura

2) Hakimin Garun Malam

3) Hakimin Takai

#Qalubale

Babban jami’in ‘yan sanda ya rasa ransa a hannun ‘yan Shi’a

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta zargi mabiya Shi’a da kashe mata jami’anta kimanin su biyar (5), cikinsu harda mataimakin kwamishinan ‘yan sanda DCP Usman A.K Umar a Abuja ranar Litinin.

#Qalubale

Design a site like this with WordPress.com
Get started