
Daga Mal Datti Assalafiy
Muna yiwa shugabannin Arewa fatan alheri, zamu yi amfani da wannan damar wajen janyo hankalin shugabannin Arewa akan tashar TV na Arewa24
A takaice dai Arewa24 tasha ce da hukumar leken asiri da tattara bayanan sirrin tsaron duniya (CIA) na Kasar Amurka ta samar ta dauki nauyi ta kawo Nigeria cibiyar Arewa/Musulunci wato Kano ta ajiye domin cimma boyayyar manufarta akan Musulunci da Musulmai
Tashar Arewa24 kyauta ne ake kallo, koma bayan wasu tashoshi irinta da sai an biya kudi, sannan ma’aikatan Arewa24 ana biyansu makudan kudi a matsayin albashi ba tare da sanin ga hanyar da kudin yake fitowa ba
Arewa24 suna gabatar da shiri da yake kayatar da ma’abota kallon tashar, daga cikin abinda suke koyarwa akwai al’adun turawa wanda ya shafi wakoki da rawa, da kokarin kore tarbiyyan yara wanda aka sani na musulunci da al’adun Hausa/Fulani, suna kuma koyar da shiga na banza, suna dusashe hasken ma’abota Littafin Allah Al-Qur’ani Maigirma
Duk wannan abinda Arewa24 sukeyi bai tayar mana da hankali ba, domin muna mayar da alhakkin hakan akan iyayen da suke barin ‘ya’yansu na kallon tashar, amma babban abinda da tayar mana da hankali har muka yanke shawaran ankarar da shugabannin mu don a dauki mataki, shine yadda yanzu Arewa24 suna dab da zasu fara koyar da ayyukan ta’addanci irin na ‘yan Boko Haram da ISIS

Sunyi tsari zasu fara nuna almajiri an daura masa rigar bomb irin wacce masu harin kunar bakin wake suke sakawa a tura su zuwa wani guri zuje su tayar da bomb su hallaka al’umma, kamar dai yadda suicide bombers na Boko Haram da ISIS ke yi, bayan wannan suna tallen yadda tsarin shirin nasu na koyar da ayyukan ta’addanci zai kasance, ta yanda akwai shugaban kungiyar ta’addanci, da kwamandojinsa da masu tsara harin kunar bakin wake, da kuma yadda ake kaddamar da harin ta’addanci a kashe mutane
Ga hotuna nan na daura, idan har shugabannin Arewa ba zasu iya dakatar da tashar Arewa24 ba saboda illoli da sharrinsu, to lallai ya zama wajibi a gargadesu a hanasu yunkurin gabatar da shirinsu na koyar da ayyukan ta’addanci, wannan ya zama wajibi gwamnatin Nigeria ta dauki kwakkwaran mataki saboda a inganta tsaron Nigeria
Iyaye suna ta korafin cewa Arewa24 sun lalata musu tarbiyyan yara, sun koya musu wake wake da raye raye da rashin kunya, to babu shakka kamar hakane zasu koyawa yara ta’addanci har a wayi gari iyaye sun fara korafi kamar yadda suke yi yanzu
Babban abinda nake so na jawo hankalin jama’a shine; yanzu fa akwai wasu abubuwa (ba zan bayyana ba) za’a nuna maka yadda zaka iya kera bomb a dakin dafa abinci na mahaifiyarka, kuma sunce kayan hada abubuwan fashewan yana gewayen gida ba masu wahala bane, to don Allah ya ake tunanin idan an fara nunawa yara kayan hada abubuwan fashewa kamar yadda ake shirin fara koyar dasu yadda za’a saka rigar bomb (suicide vest) a tashar Arewa24???

Muna kira ga shugabannin Arewa da mahukuntan Nigeria su dauki mataki akan Arewa24
Allah (T) muke roko Ya tsaremu Ya tsare mana al’umma daga sharri da makirci da cutarwan Arewa24 Amin