
Alhamis, 11/4/2019 ita ce ranar da Jam’iyyar PDP da dan takarar gwamna a Jihar Kano Engr Abba K Yusuf suka fara qalubalantar nasarar da Maigirma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi.

Wannan ya biyo bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta ayyana Gwamna Ganduje da lashe zaben. Jam’iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna Abba K Yusuf sun shigar da koken su bisa dogaro da tarin hujjojin da su ka tattara a gaban alkalai masu sauraron koke-koken zabe wadanda ke zaman su a harabar babban kotun ta Jihar kano.
#Qalubale
