Daga Umar Faruq Muhammad:

” Ina Matukar sanya Ido da kulawa da motsin Yara na, a mafi yawan lokuta kofar Gidana a kulle take, lokacin da aka sace min Yaro na nine na kaisu Makaranta shida wansa, a hanyarsu ta dawowa wasu suka biyo su,Babban a guje yasha da kyar, Barayin suka kama karamin, har yanzu kuma ba’a san inda yake ba, baya cikin 9n da aka samu a Anambra. ”
Wannan Jawabin Shugaban Kungiyar Iyayen da aka sacewa Yara ne, yayi wannan jawabin ne a taron da JTI ta shirya, yana nuna takaicin sa game da Mutanen dake rufe Ido suce ai sakacin Iyaye ne kesa a sace ‘Ya’yan su.
Nima na yarda da wannan magana tasa, domin ko kwanaki Yarinya Aisha da aka sace aka kuma samu gawarta ai daga Makarantar Islamiyya ta dawo ita da yayarta aka tafi da ita yayar ce kawai ta dawo gida.
A fahimta ta matukar Mutum bazai fadi kalmar tausasawa ga irin Iyayen nan ba zaifi sauki ya kulle bakin sa, bai kamata yafadi abinda zai kara musu zafi kan zafin da suke ciki ba.
Qalubale@gmail.com
