
Wata kotun daukaka kara dake Kaduna inda Abba K Yusuf ya daukaka kara ta yanke hukunci cewa Abba K Yusuf shine halattaccen dan takara a Jam’iyyar PDP
Wannan ya biyo bayan qalubalantar da mai neman takara Ibrahim Ali Amin ya kewa Abba K Yusuf din a wata babbar kotun tarayya a Kano inda alkalin kotun ya yanke hukuncin rashin halattar Abba K Yusuf din sakamakon zargin rashin aiwatar da zaben fidda gwani.
