
YAU da safe Premium Times ta wallafa labarin ‘yan Boko Haram sun kashe sojan Najeriya har 15, tun jiya jaridar The Punch suka bada bayanin ‘yan BH sun karbe wani sansanin soja a Magumeri kusa da Maiduguri tsawon awa hudu. Sun kwashe duk makamai a sansanin, sun yashe sauran kayan yaki.
Da safiyar nan BBC suka rawaito labarin yadda yan fashin daji suka yi wa mutanen Dan gurgu na kasar dagacin DanSadau su 30 kisan gilla.
Kafin wannan Daily Trust ta yi rahoto cewa miyagu akan babura sun je Safana da Batsari a jihar Katsina sun kashe mutane har yanzu ana lissafin adadi. A tsakanin wannan lokaci aka sace Magajin Garin Daura a Dauran a kofar gidansa, akan hanyar Abuja kuma aka sace shugaban hukumar UBEC na kasa da ‘yarsa aka kashe direbansa. Har gida aka je aka kashe mai gadin Bafarawa, aka gudu da wata karamar yarinya.
Kowa ya sani da Filato da Binuwai da Taraba kai da ko ina a arewa ba lafiya.
A wata kidddiga da jaridar THE Punch ta yi, wacce ta samu daga ‘yan sanda ga link din https://punchng.com/1071-killed-685-kidnapped-in-first-quarter-of-2019-ig/amp/, sun ce a cikin wata uku daga Janairu zuwa Maris 2019 kacal, an kashe mutum dubu da 71, an sace 685 a Najeriya, abin yafi muni a arewa, a arewan kuma jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da Sakkwato da Kebbi da Jigawa da Kano.
Sam-sam ban gamsu da matakan da gwamnatin jam’iyyarmu ta APC ta Muhammadu Buhari take dauka ba. Ra’ayin da Rabiu #Biyora yake cewa wai mutanen arewa su hada kansu a yaki wannan abin ban gamsu ba. Wa ye yake da soja da ‘yan sanda da bindiga da kudi da kasar da kasashen waje? Ku ce min Buhari kawai, to ku sani aikinsa ne. Shi ya nada kowa, in wani ya gaza shi zai sallame shi. Don me za a kyale kowa sai cin karensa yake ba babbaka? Shugaba Muhammadu Buhari fa dole ya farka, kuma dole ya katse komai ya dawo ya sauya fasali.
A kasar Srilanka fa da ‘yan ta’adda suka kashe mutum 400, tuni aka kori sufeto janar na yan sanda da ministan tsaro, shi kansa shugaban kasa kujerarsa rawa take yi, komai na iya faruwa.
A nan ma Africa kasar Mali, gaba dayan gwamnatin sauka ta yi saboda an kashe mutum 160 kuma an gaza shawo kan lamarin.
Haka kuma ban amince da ra’ayin Ibraheem A. Waziri ba, cewa system din ne matsalar. Ina son tabbatar muku, matsalar ta mutanen ce, shugaba Buhari ya gwada cire su, ya kori wasu, ya zakulo masu nagarta ya basu dama, ya ga aiki da cikawa. In ba zai iya ba, shima ba lallai ba tilas.
TSARON NAJERIYA SHI NE FIRST
Daga Bello Muhammad Sharada
