
Duk lokacin da Mallamai ke bayani game da wani tanadi na Rahma da Allah yayi wa Muhsinai cikin bayin sa zakaji Mutane suna nuna zumudin kaiwa ga Wannan Rahmar.
Abin takaicin shine sam bamu da karsashin aikata ayyukan dake Jagorancin kaiwa ga Rahmar.
Daga shekaranjiya duk wanda yashiga Kasuwannin Kano siyan kayan Masarufi don tanadin Azumi zai tarar da canjin Farashi ta hanyar karuwa fiye da satin da yagabata.
Abin tambayar shine ta wacce hanya farashin ke karuwa a duk watan Ramadhan? Shin ba watan Ramadhan bane watan da Rahmar Allah ke samuwa?
Meyasa Yan Kasuwa Musulmi suke tsawwalawa Yan uwan su a wannan watan? Shin a haka muke tunanin Allah zai bamu tasa Rahmar?
Yanzu don Allah bamajin Kunya in Ramadhan ya wuce sai kuma mu sauke farashi?
Gaskiya Musulmin mu na wannan zamanin muna da Matsaloli, da kanmu muke kuntatawa junan mu.
Daga Umar Faruq Muhammad
