GA A INDA MATSALAR TA SAMO ASALI

Daga Adam M Panda:

A dan kwarya-kwaryan binkicen da na gabatar mun gano wasu daga cikin musabbabin da suke sauya dabi’un matanmu daga abokan rayuwa zuwa abokan fargaba

Matsalolin sune
Kawaye
Wayoyi
Litattafai
Kalle-kalle

1. KAWAYE
Hakika yin mu’amala da matanmu da ‘ya’yanmu keyi da gurbatattun Kawaye yana matukar tasiri wajen lalata tarbiyyar da muke dora matanmu da ‘ya’yanmu akai, don haka ya zama. wajibi garemu mu tantance su waye kawaye iyalanmu a gidajenmu da kuma makarantun ‘ya’yanmu

2. WAYOYI
Ba makawa wayoyin da iyalanmu kanyi amfani da su na da matukar tasirin wajen kyatata tarbiyyar iyalanmu ko gurbata ta.

3. LITATTAFAI
A wannan yanayi da muke ciki karance-karancen ko sauraron masu karanta Litattafan soyayya wani bangare ne na wasu daga cikin iyalanmu, wanda wani lokacin ma zaka iya cewa kaso ne mai yawa a lokutansu, harma wasunsu suna fifita wadancan karance-karance fiye da hakkokin da suka rataya akansu na mazajensu ko iyayensu, da dama wasu mutanen sun sha yin korafin cewa “Iyalensu sun sha yi musu asarar dukiya sakamakon shagaltuwa da irin wannan karance-karance”

4. KALLON FINA-FINAI
Tabbas wannan dabi’a ma tana matukar gurbata tunanin iyalanmu, wanda za kaga Uba ko Mai gida ya sayawa iyalansa kayan Kallo amma babu ruwansa da sanin irin tashoshin ko kasansunan da suke kallo wanda lokuta da dama, Makiya Allah nayi amfani da wannan dama wajen haska gurbatattun fina-finan da zasu iya gurbata tunanin iyalanmu.

A karshe da wannan da binkice nakeso nayi amfani wajen tuna mana Hadisin Shugaba S.A.W wanda yake mana
“KULLUKUM RA’IY WA KULLUKUM MAS’UULUN AN RA’IYYATIHI”

MA’ANA
Dukkanku Makiyayane kuma kowa abin tambayane akan kiwon da aka bashi

(Sadaqarrasulul-kareem)

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started