
Gamammiyar kungiyar cigaban al’umma a Najeriya mai suna Coalition of Civil Society Organisations sunyi wata zanga-zanga ta lumana ranar Juma’a 13/9/2019 a Kaduna.
Kungiyar tayi kira ga Gwamnatin tarayya tayi gaggawar rufe hanyar zirga-zirga tsakanin Abuja-Kaduna a jirgin kasa, wannan ya biyo bayan yadda masu garkuwa da mutane suka maida hanyar mota Abuja-Kaduna wajen cin karansu ba babbaka.
Kungiyar tace duk wani mai fada a ji daga kan manyan ma’aikata zuwa manyan yan kasuwa da manyan ‘yan siyasa da manyan sojoji sun koma tafiya a jirgin kasa domin gudun haduwa da ‘yan garkuwa da mutane.
Jirgin kasa kuma anyishi domin talakawa su amfana amma yanzu ya gagari talaka, gashi kuma yayi tsada, masu kudi sun saye tikiti sun bar talakawa dole subi hanyar mota da ‘yan garkuwa ke sintiri, inda suke rasa rayukansu yayin da akayi garkuwa dasu saboda basu da kudin da zasu iya fansar kansu.
Kungiyar tace ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta rufe hanyar jirgin kasa domin manyan jami’an gwamnati su dinga bin hanyar mota saboda suna tafiya da jami’an tsaro da jerin gwanon motoci wanda yin hakan yana rage sintirin ‘yan garkuwa da mutane akan wannan titin inji daya daga masu zanga-zangar Yusuf Amoke.
Qalubale@gmail.com
