Daga Datti Assalafiy:

Rundinar sojin hadin gwiwa na kasashen dake iyaka da tafkin Chadi Multinational Joint Task Force (MNJTF) sun samu nasaran hallaka wasu daga cikin manyan kwamandojin yakin kungiyar Boko Haram/ISWAP reshen ISIS na duniya
Wannan nasara ta biyo bayan ruwan wuta da dakarun sojin hadin gwiwar sukayi ta sama da jiragen yaki da kuma sojojin kasa ‘yan kundunbala a wani katafaren yanki da ake kira Tumbus dake tafkin Chadi, wanda yayi sanadin hallakar ‘yan ta’adda masu tarin yawa da kwamandojin yakin su
Sahihan bayanai ya nuna cewa wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun tsallaka sun gudu zuwa kasashen Sudan da Kasar Afirka ta tsakiya, sannan manyan kwamandojin yakinsu a kalla guda 7 suka hallaka sakamaon ruwan wuta da dakarun sojin sukayi ta sama da kasa
Ga sunayen manyan kwamandojin yakin Boko Haram/ISWAP da suka hallaka kamar haka
1-Abba Mainok
2-Bukar Dunokaube
3-Abu kololo
4-Abor Kime ( balarabe ne ‘dan kungiyar ISIS da yake bawa Boko Haram/ISWAP horo).
5-Mann Chari.
7- Dawoud Abdoulaye (‘dan Kasar Mali)
7- Abu Hamza.
Wadannan kwamandojin ‘yan ta’adda da aka hallaka sune suke lura da ayyukan ta’addanci a yankin Tumbus dake tafkin chadi, ba lallai ne ya zama asalin sunayensu ba, amma shine sunan da ake musu lakabi dashi a yankin, rundinar sojin tana kokarin tattara dukkan bayani a kansu
Wannan sanarwan ya fito a yau juma’a 20-9-2019 daga mukaddashin mai magana da yawun rundinar sojin Nigeria Kanar Sagir Musa
Allah Ka kara tabbatar da nasara akan ‘yan ta’addan Boko Haram
Qalubale@gmail.com
