YAWAN JAMA’A MASU AMFANI SHINE ABIN ALFAHARI

Daga Comrade Auwalu Mudi Yakasai.
Juma’a 22/09/2017.
(Juma’a, 1 Muharram 1439 AH).

A shekarun baya an san al’ummar Hausa/Fulani a ko ina a duniya wajen juriya da jarumtaka da gaskiya da rikon amana da sadaukar da kai wajen gwagwarmayar neman halak da neman ilimi dadai sauran halaye masu kyau.
Abin takaici a yanzu da muka kara yawa sosai kuma muke bukatar irin wadancan halaye masu kyau sai abin ya canja.
A yau wasu daga cikin mu sun shahara wajen girman kai da son zuciya da lalaci da karya da kyashi da alfahari da hassada da cin amana.
Wasu daga cikin matasan mu babu abinda suka iya sai tumasanci da fadanci da kwadayi da munafurci. Babban abin haushin ma sai ka ji matashi yana alfaharin cewa shi ya fi karfin yayi wata karamar sana’a ko da kuwa da ita mahaifinsa ya rayu, kuma ita aka gada a gidansu. Amma wannan kuma bai hana shi yawon roko da maula a wajen masu irin wannan sana’ar ba.
Sakamakon haka duk sana’oi da aka san mu da su a gidajen mu kusan duk sun durkushe, wadansu ma an daina su baki daya, wanda hakan ya kara haifar mana da talauci da zaman banza.
Duk wanda ya zagaya Najeriya sosai zai fahimci cewa a yanzu matasan mu kadan ne suke iya fita sauran jihohi neman halak dinsu. Mafiya yawan matasan mu suna zaune ne a lunguna babu abinda suke sai surutan banza da musun siyasa da zargin cewa wai ba a taimaka musu kawai saboda mutuwar zuciya da son banza. Wasu daga cikinsu ma har sukan shiga shaye-shaye da bangar siyasa da sace-sace dadai sauran dabi’u marasa kyau, maimakon su maida hankali wajen neman ilimin addini da na zamani wadanda zasu taimake su a nan duniya da kuma lahira. Wadansu kuma ma iyayensu da yayyensu ne abokan gabarsu kawai saboda suna kokarin nuna musu gaskiya. Babu biyayya da ladabi ga iyaye ballantana ma a kyautata musu.
Wani abin al’ajabi ma shine yadda zaka ga matashi kai kana jin tausayin sa, amma shi kuma yana jin haushin ka. Kullum burinsu shine su sami kudi su more rayuwa duk da yake basu dauko hanyar da zata kaisu ga hakan ba.
Babu shakka matukar muka ci gaba da zama a irin wannan hali na rashin sanin ya kamata, to tabbas zamu cigaba da rayuwa cikin damuwa da koma baya da talauci da rashin zaman lafiya.
Gaskiya ne muna da yawa kwarai da gaske. Amma yawan namu ba zai amfane mu ba sai mun jajirce wajen dora rayuwar mu akan tafarki madaidaici.
Lokaci yayi da zamu farka mu yi amfani da yawan da muke da shi don mu amfani kanmu da al’ummar mu.
Wajibi ne kowannen mu babba da yaro da mai arziki da talaka da shugabanni da mabiya da malamai da almajirai kowa ya gyara zuciyar sa kuma mu kyautata niyya a dukkan al’amuran mu idan har muna son Allah (SWT) Ya dube mu da idon rahama.
Allah (SWT) Ya sa mu gane gaskiya, Ya kuma bamu ikon bin ta.

Qalubale@gmail.com

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started