
Kungiyar kwadago tace ya zuwa yanzu babu lokacin da ma’aikata zasu sa rai da fara karbar sabon tsarin albashi na kasa baki daya.
Wannan ya biyo bayan komawa da hannun agogo baya da gwamnatin tarayya tayi na sake fasalin kwamitin da ta nada domin daidaitawa da gamammiyar kungiyar kwadago ta kasa.
Fiye da watannin shifa (6) da suka wuce majalisar tarayya ta amincewa gwamnatin tarayya ta biya mafi karancin albashin na Naira dubu talatin (#30.000) ga ma’aikatan kasarnan baki daya, bayan an shafe fiye da shekara daya (1) ana fafatawa wajen nemo yawan albashin da yafi dacewa ga ma’aikatan, daga baya kuma shugaba Buhari ya sa hannu a fara biya.
Abin mamaki duk da wannan lokaci da aka shafe na kusan shekaru biyu (2) da tattaunawa da sahalewar majalisa da sahalewar shugaban kasa amma abin yaci tira, domin har yanzu ma’aikata na dandana wani salon mulki na yaudara a hannun wannan gwamnati, inda shugabannin kwadago suke cewa tunda suke basu taba ganin irin wannan mulkin mallaka da yaudara ga ma’aikata ba sai a wannan karo.
Babban abin lura shine, yan kasuwa tunda fari da sukaji za’a karawa ma’aikata albashi suka karawa kayayyakin masarufi na yau da kullum kudi kuma har zuwa yanzu kudaden kayayyakin sai kara karuwar sukeyi.
Muna fata Allah ya kawo karshen gasawa ma’aikata aya a hannu da gwamnatin Najeriya keyi.
Qalubale@gmail.com
