
Munyi Allah wadai da kamfanin bada hasken wutar lantarki a Kano, wannan kamfani ya durkusar da harkokin yau da kullun na al’ummar Jihar Kano.
Yanzu haka a kowace unguwa bai wuce a basu hasken lantarki na awa 2 zuwa 3 ba a kowace rana, kuma wata na karawa a kawo takardar biyan kudin wutar, mun rasa dalilin da zai hana asa wa kowa meter.
Akwai alamun yin zagon kasa ga gwamnatin Buhari da wannan kamfani yakeyi, domin muna samun labari cewa, a sauran jihohin kudancin kasar suna samun wuta sosai, don haka muna kira a chanja mana masu sayar da wuta a wannan bangare namu na Arewa.
Qalubale@gmail.com
