Daga: Fa’izu Alfindiki Kano:

SARKIN BIRNIN KANO MUHAMMADU SANUSI YA KASA ZUWA SAUKAR KARATUN JAMI’AR YUSUF MAITAMA SULE A KANO, SABODA SARKIN BICHI DA RANO DA GAYA SU NA WAJEN
Cikin wata irin dimuwa da gigicewa Sarkin cikin birnin Kano Muhammadu Sanusi II, ya juya tare da ‘yan rakiyar sa daga shiga harabar Jami’ar Yusuf Maitama Sule dake Kano, masu magana dai sun ce babban dalilin da yasa mai martaba sarki ya arce saboda halartar Sarakuna masu Daraja Ta Daya, daga Masarautun Bichi, Gaya da Rano, wajen bikin yaye dalibai na farko a Jami’ar.
Idon kowa ya yaga yadda kawai aka ga motar Sarkin ta tsaya kan titi ta hada wani uban cunkushewar hanya, Sabo da ga dukkan alamu shi’kan sa dreban ya nimauce, sabo da watakila yayi ido biyu davsarkin bichi, ko na rano dana gaya ko kuma na karaye yaga kwarjini a idanun sarakuna masu daraja, lokacin da a ka ga motar Sarkin ta juyo da gudu, ba ma tare da tsayawa ‘yan rakiyarsa ba. Sai ma daga baya motar fadawansa ta same shi ya kusa karasawa fadarsa.
Wannan irin halin da ya nuna ya batawa mutane rai da yawan gaske a waje taron. Saboda an ji kide-kiden motarsa ta fada da kuwa bushe bushen kakaki, amma sai ya yi biris ya juya ba ma tare da sanar da shugannin Jami’ar ba.
A na ganinsa ya koma gida, a na zuwa Kofar Kwaru ya sauka cikin fushi yana sambatu ya shige gida a kafa. An ce an gan shi ya na ta yi wa fadawansa fada cikin fushi, wai saboda me za su bari sai da a ka kusa zuwa wajen taron sannan za su gaya masa akwai Sarakun ragowar Masarautun a wajen taron.
Mutane an gan su suna ta maganganu kan wannan abinda Sarkin ya yi. Wasu su na cewa ya yi daidai. Wasu kuma suna cewa hakan bai dace ba ko kadan. Su na ta cewa Sarkin ya dau wannan dambarwa a matsayin gaba da kiyayya.
Babban abin da ya ba mutane haushi ma shine, da yake an sanar da zuwan Sarkin a wajen taron, amma ya watsawa hukumomin Jami’ar kasa a ido. A na dai sauraron ganin abinda Sarkin zai yi wa fadawansa dalilin wannan “katobara” da ya ce sun masa.
MU NA JI MU NA GANI MU NA KUMA SAURARO. IDO NE KAWAI NA MU.
