Rikicin Masarauta a Kanon Dabo

SIYASAR KANO SAI DAN KANO!

  • Daga Musa Muhammad Gama:

Lokacin da mai girma Sardaunan KANO Malam Dr. Ibrahim Shekarau yake gwamna Kanawa suka zargeshi da wuce gona da iri wajen kyautatawa Masarauta, domin a karkashin jagorancin marigayi Alh Dr. Ado Beyaro ya kafa kungiyar adaidaita sahu tare da sayawa hakiman KANO mota kirar Prado, a wance zamani Sardaunan yasha suka a wajen talakawa suna zarginshi da karawa mai karfi_ karfi. Lokacin da aka bashi muqamin Sardaunan KANO sukace sayen sarautar yayi.

Sabon Gwamna sabon Sarki, abinda magoya bayan kwankwaso, salon kanfen da suka fito dashi, bayan yazama gwamna masarautar KANO tashiga Next level, daga bisaniya Bayan rasuwar Marigayi Alh Ado Bayero, kwankwaso ya jagoranci Nada sabon Sarki Wanda haka ya jagoranci zanga_zangar da kone_kone tayoyi a kan titinan cikin gari, Wanda sai daga baya al’amura suka daidaita.

Dr.Abdullah Umar Ganduje, a farko tenure an sami fahintar juna tsakanin Gwamnatin KANO da Masarauta, Amman a tafiya zango na biyu, aka sami ‘baraka Wanda hakan ya janyo gwamna ya rage power Masarauta zuwa kashi biyar. A wannan karon shikuma Ganduje ake zarginshi da raba kan al’uma tare da haddasa rikici a fadin jihar KANO.
Shin wai mu Kanawa bamu da gwanine?

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started