Daga Jamilu Muhammad Maijakai:

Hukumar karota tayi Nasarar Chafke dan karotar Bogi a kasuwar kantin kwari dakenan kano
Shi Wannan dan karotar Bogi mai Suna Sulaiman Haladu an kamashi ne a kasuwar kantin kwari lokacin da yake gudanar da dabi’arsa ta karbar kudi a hannun drebobin motar da suke kokarin fita daga kasuwar
Bincike yanuna cewar shi dan karotar bogin dan asalin jihar Katsina ne mai kwana a cikin kasuwar ta kwari
Dan karotar bogin yace sun Dade suna gudanar da Wannan al’adar tasu kuma dubunsu bata taba cikaba sai a Wannan karin
Tun farko dai Hukumar ta karota ta karbi korafe korafe ne daga wasu daga cikin yan kasuwar ta kwari,
Inda Hukumar ta tura jami’anta na sirri dan gano da kuma bankado masu aiwatar da Wannan dabi’a
Hukumar ta karota ta mikashi zuwa Hukumar yan sanda dake nan Kano dan fadada bincike
In kunne yaji jiki ya tsira
Jamilu Muhammad Maija
