
A SHIRIN ZAMAN ‘YAN MARINA
An gayyace ni tattaunawa ta musamman ta awa guda a gidan Rediyon FM RAHAMA 97.3 da ke KANO, a safiyar gobe Talata 28 Janairu 2020 da misalin karfe goma na safe.
Za a tattauna ne akan
YADDA ZA A CI RIBA DA GAJIYAR ZABE. Kusan shekara guda da yin zabe, an gama duk wata sharia, sannan an gama duk wani sabon zabe. Yanzu mulki da jagorancin alumma ne ya rage, da yadda zasu sha romon dimokuradiyya.
Za a yi muhawara kai tsaye da tambayoyi daga masu sauraro kuma suke son yin tsokaci akan batun. A yi sauraro lafiya
Naku Bello Muhammad Sharada
NAGODE
