Daga Faizu Alfindiki:

Tarihin siyasar Kano ba zai manta da zabukan da Kwankwaso ya jagoranta ba musamman na kananan Hukumomi a 2014 da babban zabe na 2015.
A 2014 jam’iyyar da Kwankwaso ke yi ita ce ta lashe gaba dayan Shugabannin kananan Hukumomi 44 da Kansiloli sama da 400, a yadda Kano take in dai lissafi na hankali za ayi amfani da shi za’a san hakan ba zai yiwu ba.
Kowa ya san yadda Kanawa suka fi muhimmantar da zaben shugaban kasa akan na Gwamna, amma a rubutun Kwankwaso
na 2015 yawan kuri’un da aka kada a zaben Gwamna sun fi na shugaban kasa, duk wanda ya kalli hakan zai tabbatar rubutu aka yi amfani da shi ba ainihin abinda jama’a suka zaba ba.
Kaf siyasar Nijeriya babu inda aka taba samun an yi zaben fidda gwani cikin gidan Ubangidan daya daga cikin ‘yan takara, amma a 2018 da Kwankwaso ya dawo PDP ya yi amfani da
karfin tsiya ya shirya zaben fidda Gwani a gidan sa kuma ya rubuta sakamakon da ya rinjayar da yaron sa, ya take su Malam Salihu Sagir Takai, Jafar Sani Bello da Sadiq Wali.
Yanzu wadannan abubuwa da Kwankwaso da Kwankwasiyya suka aikata suna da wani suna da ya wuce zalunci?
Me yasa mutanen da ya zalunta ba su bayyana bacin ransu ba ta hanyar tsinuwa ko mummunan fata ga Kwankwaso?
A baya bayan nan ma an jiyo shi yayin da yake hira da wata ‘yar jarida, yake cewa Salamatu kalli ido na da kyau, na yi miki kalar wanda zai ci zabe a kwace masa!
Kwatsam ran nan muka jiyo shi a rediyo yana ta Allah ya isa kuma yana cewa zalunci ba kyau. Duk mai zalunci ba ya nasara.
Yayin fushi, jarumi shine wanda yake mallakar zuciyar sa, Akasin hakan kuwa RAGWANTA ce a bayyane.
Da wanan za mu iya kiran Kwankwaso da Ragon Dan Siyasa, shi ba Jarumi bane!
Qalubale@gmail.com
