BUBA GALADIMA YA ZAGEMU ‘YAN AREWA

By: Abdullahi Sarkin Yakin Apc

Yanzun nan kammala sauraran jawabin da Buba Galadima yayi a cikin bidiyo, inda ya game ‘yan Arewa gaba dayanmu ya kiramu da kalmar shashashu saboda munki tayar da zanga-zangar kamar yadda ‘yan kudu sukayi

Sannan bai tsaya anan ba, Buba Galadima yaci mutuncin Malamin mu shugaban Majalisar Malamai na duniya a kungiyar Izala Sheikh Sani Yahya Jingir, inda ya tuhumi Malam da kokarin bawa shugaba Buhari kariya

Buba Galadima yace su ‘yan Arewa babu abinda suka iya sai batun addini, ana taba mu sai mu kawo addini

Hakika na kara fahimtar cewa wannan rikicin akwai sa hannun manyan miyagun ‘yan siyasa a Nigeria, ba damuwarsu barnan da ‘yan ta’adda masu zanga-zanga ENDSARS sukayi ba, damuwarsu shine mutane 30 da suke karyan cewa wai sojoji sun kashe

Buba Galadima ka zagemu shashashu ba zamu rama ba, amma hakika mu ba shashashu bane, Insha Allahu su Buba Galadima ba zaku ci nasara ba, kuma insha Allahu shugaba Muhammadu Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa lafiya

Yaa Allah Ka haramta wa ‘yan jari hujja zuwa kusa da madafun ikon Nigeria

qalubale.news.blog

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started