
Bayanai dake fitowa daga bakin ministan ayyuka da gidajen Najeriya Babatunde Fashola yace, titin da gwamnatin tarayya ke ginawa daga Abuja zuwa Kano, ba zai kammala ba sai shekarar 2025, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na wasu kusoshin gwamnatin tarayya a Kaduna.
Gidan radio na BBC ne ya bayyana wannan labari a shafinsa, an fara gina wannan titi a shekarar 2018 karkashin gwamnatin shugaba Buhari bisa tabbacin za’a kammala shi cikin sauri duba da irin lalacewar da yayi, ga shi kuma yana lakume rayukan al’ummah sakamakon haddura dake faruwa

Su ma masu garkuwa da mutane su na amfani da wannan dama wajen tare hanya su sace mutane ayi garkuwa da su domin karbar kudin fansa, gwamnati ta kiyasta kashe wa wannan titi kudi naira biliyan dari da hamsin da biyar #155bn.

A gwari-gwari dai zamu iya cewa, har sai Buhari ya kammala wa’adin mulkin sa kafin a kammala titin, duk da matsalolin da titin ke haifarwa a wannan yanki na Arewa ta hanyar rasa rayuka, sace mutane, fashi da makami da ake yi a hanyar, amma sai jan kafa akeyi wajen kammala shi.
Idan gwamnatin shugaba Buhari dan Arewa ta kasa kammala wannan aikin titi a wannan lokaci, wace gwamnati ce zata taimakawa Arewa wajen kammala shi?
