Matasanmu na social media sun fara dafe madafun iko

Sau da yawa a yayin zama da mukeyi da jagororin mu, suna fada mana cewa, ya zama wajibi mu tashi mu nemi madafun iko kodai a matakin jam’iyya ko na mulki, daga dukkanin alamu matasan sun yunkuro domin yin amfani da shawarwarin jagororin namu.

Wata rana Sen Ibrahim Shekarau yana fada mana cewa, dukkanin shugabannin da suka mulki kasar Najeriya a lokacin da suka karbi ragamar mulkin, matasa ne, wasu ma idan an kwatanta shekarun mu a wannan lokaci da shekarun su a wancan lokacin da suka karbi madafun iko.

Za’a iske mun girmesu, saboda yawancin su, sun karbi ragamar mulki suna da shekaru 30 ne, ba sukai 40 ba, da alama wannan yayi wa matasa kaimi domin fitowa a wannan lokaci wajen neman kujerun mulki daban-daban, daga siyasar social media ta rikide zuwa siyasar mulki.

Muna rokon Allah, ya dafa wa duk wadanda suka sami nasara wajen karbar tikitin shiga zaben kananan hukumomin su, wadanda basu sami wannan damar ba, muna rokon Allah, ya canja masu da mafifi cin alkhairi.

Daga karshe ina yiwa dan uwan abokin gwagwarmaya Auwal Lawan Aranposu addu’a Allah yabada nasara a zaben da za’a shiga kuma ina rokon Allah, ya bashi Ikon kwatanta adalci a karamar hukumar Nassarawa da sauran yanuwa da abokan arziki da suka sami irin wannan dama.

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started