Ra’ayin Mawallafi: Barazanar da Kudancin Najeriya ke wa Arewa

Yankin Arewacin Najeriya da ke da fadin kasa da arzikin al’ummah da ma’adinai da ke jibge a karkashin ilahirin Arewa wanda shugabannin mu su ka kasa amfani dashi wajen ciyar da yankin gaba, yana samun barazanar wariya daga sauran sassan kasar.

Yanzu dai ta tabbata Arewa bata da katabus a idon abokan zamanta na sassan kasar, masamman Kudanci, wane dalili yasa motsi kadan ake mana kallon kaska duk da irin dimbin al’ummah da fadin kasa da kuma ma’adinai dake jibge a karkashin kasar ta Arewa?

Shugabannin mu na Arewa da suka rike mulkin kasa a wannan karni basu kwatanta halin shugabannin baya ba, basu maida hankali wajen gina al’ummah da tattalin arzikin Arewa ba, shine dalilin da talauci da jahilci suka mamaye Arewa, wannan ya haifar mana da rashin tsaro.

Ba wani motsi da dan Arewa zai yi sai ya sami qalubale daga yan Kudu wajen neman a raba kasar, sun gaji da zama da mu, wannan ya zama kamar wata tsokana da akewa yan Arewa.

Badan lalacin matasan mu ba da rashin maida kai wajen neman ilimi, Arewa daidai take tayi gogayya da kowace nahiya, amma mun kasa daidaita kawunan mu, wannan kuma ya biyo bayan rashin tallafawa daga mahukunta, kowane jinsi yana kokarin tallafawa dan uwansa amma banda hausawa.

Mun zama abin dariya a idon duniya, sai binmu ake ana kashewa kamar beraye, yan kudu su kashemu saboda munje jihohinsu neman abinda zamu rufawa kanmu asiri duk da suma suna shigowa jihohin mu neman kudi, musulunci ne ke mana jagora wajen zama da kowa lafiya a yankunan mu.

Maganar raba kasa taki ci taki cinyewa, wancan mai da yan kudu ke tinkaho dashi, kudadenmu ne aka dauka daga Arewa da muke noma gyada da auduga wajen hakar sa, sai gashi ya zama abin tinkaho da barazana garemu.muna da mai da iskar gas da gwal da glass da sauran ma’adinai a Arewa.

Muna da mai da iskar gas da gwal da glass da sauran ma’adinai a Arewa, meyasa shugabanninin mu na Arewa suka kasa amfani da wannan damar wajen hako wadannan ma’adinai, ko ba komai zamu fita daga talauci, jahilci da rashin tsaro, matukar muka zama masu cin gashin kanmu.

Ba fata muke a raba kasar ba, amma dai a sani cewa idan ma ya kama sai an raba din, ya kasance muna da madafa, abinci da muke nomawa kadai idan an tsaya akansa ya ishemu rayuwa, amma sai gwamnatocin mu sun dage wajen tallafawa aikin tare da jan talakawa a jiki da basu kulawa.

Kulawa na shawarwari da bude mana idanu wajen yasar da lalaci da zaman kashe wando ta yadda zamu dogara da kanmu, ya zama wajibi gwamnonin Arewa su dauki wani tsari na bai daya wajen tabbatar da wannan manufa idan har muna son Arewa ta zauna da gindin ta.

Duk wasu shugabanni daga Arewa da suka taimaki Arewa da ma wadanda basu taimaki kowa ba sai kawunansu, sun sha kwarzaba daga yankin kudu, duk da cewa suma yan Kudun sun yi mulki amma ba wanda ya kwarzabesu, amma duk lokacin da dan Arewa ke mulki sai yasha qalubale daga hannun su.

Mun san shugabannin mu basa mana adalci duk da dauke kai da mukeyi daga garesu, tunanin su din namu ne kuma sun fito daga cikin mu, amma su a karan kansu basa duba haka wajen taimakawa yankin Arewa, muna gani wadanda ke matsa masu lamba sune yan lele a wajensu, mu kuma ko oho.

Shin wannan zai sa a tuna da su anan gaba kamar yadda ake tunawa da magabatansu wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen kawowa Arewa abinda har zuwa yanzu muke alfahari dashi, irin su Sardauna da Tafawa balewa, wadanda har suka koma ga Allah basu tara dukiya domin amfanin kansu ba?

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started