
Gwamnatin shugaba Buhari tayi kokari wajen shimfida bututun iskar gas zuwa Kano, bazamu fasa fadan ayyukan alkhairi da gwamnati ta kawo ko take shirin kawowa arewa ba, haka kuma bazamu daina fadar inda shugaban yayi kuskure ba, masamman a harkar tsaro.
Shima muna sa rai shugaba Buhari zai ji koke-koken al’ummah a gyara domin rashin tsaro a arewa yayi muni dayawa fiye da kowane lokaci, anyi wa manoma yakan rago a Borno wanda ake tunanin yawansu yakai mutane 43 zuwa sama a cewar wasu kafafan yada labarai.

Kungiyar ta’adda ta Boko Haram ta dauki nauyin aikatawa, haka kuma an sace yara a makarantar kwana ta kimiyya da fasaha a Kankara jihar Katsina, wanda yawansu yakai 333 a cewar gwamnatin jihar ta Katsina, inda wasu kafafan yada labarai sukace sunkai 600.
An sami rashin daidaiton bayanai tsakanin gwamnatocin biyu ta jihar Katsina da ta tarayyar Najeriya wajen fitar da sanarwar yawan yaran da aka sace, inda gwamna Masari ke ikirarin su 333 ne inda kuma kakakin yada labarai na shugaba Buhari Garba Shehu yace su 10 ne
Da fari dai ana zaton masu garkuwa da mutane suka sace yaran domin neman kudin fansa, amma daga baya kungiyar ta’adda ta Boko Haram ta dauki nauyin sace yaran, amma gwamnatin jihar Katsina ta karyata hannun kungiyar Boko Haram inda tace tana tattaunawa da wadanda suka sace yaran.

Babban abinda ya bada mamaki shine, an sace yaran a yayin da shugaba Buhari ya fara hutu a mahaifarsa Daura ta jihar Katsina, kamar kilometer 190 tsakanin inda yake a Daura da inda aka sace yaran a Kankara, a yadda masana suka bayyana, wanna ba karamin cin fuska bane.
Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa yaran an korasu ne cikin daji a cikin wannan dare kamar yadda ake kora shanu, sunyi tafiyar kafa har wayewar gari amma babu wata tirjiya da suka samu daga jami’an tsaro.

Masana sunce jiragen sama na leken asiri da Najeriya ke amfani dasu wajen gano inda mahara ko yan ta’adda ko masu garkuwa da mutane ko duk wani nau’i na ta’addanci basa iya tashi da daddare, karfe 6 na yammacin kowace rana ake sauke su kasa sai wata safiyar kafin su sake tashi
Idan hakane, ta yaya za’a iya gano mahara ko yan ta’adda yayin da suka aikata barna a cikin dare, ma’ana dai sai sunkai inda zasu buya kafin daga baya jami’an tsaro su fara nasu bincike wanda zai basu wahalar gaske kafin su fahimci inda suke boye.
Da alama suma maharan ko yan ta’addan suna da wannan bayanan sirrin a hannunsu, shine dalili da yasa suke cin karen su ba babbaka a cikin dare inji wani mai sharhi a talabijin na farin wata wanda ke watsa wani shiri na Idon Mikiya a gidan radio na Vision fm 92.5MHz
Dan jarida Shu’aibu Mungadi yace, shin wadanda suka siyo wadannan jiragen sama masu leken asiri ba su san jiragen basa iya tashi cikin dare domin gano mafakar ayarin yan ta’adda bane kokuwa menene dalili da yasa suka siyo jiragen?

Lallai ya kamata zuwa yanzu, shugaba Buhari ya aje duk wani aiki na raya kasa ya debi kudin ya zuba a harkar tsaro a siyo jiragen saman leken asiri na zamani domin ayi maganin ta’addancin dake faruwa a kasa baki daya,.
Duk wani aikin raya kasa da gwamnati zata aiwatar bazai isa ga al’ummah ba idan ba tsaro, ballantana su more ko su sharhi romon dimokaradiyya, duk da haka zamu yabawa shugaba Buhari indai a wannan karin zai waiwaya arewa ya magance mana abubuwan da suka damemu.

Masamman fatara da talaucin da suke sa matasa shiga harkar ta’addanci a yanki arewa, ko shakku babu tattalin arewa ya karye rugu-rugu, aikin bude tashar ruwa ta tsandauri da jawo bututun iskar gas zasu taimaka.
Haka kuma ayi kokari a jawo teku zuwa arewa, a hako man fetur da iskar gas da sauran ma’adinai irin su zinare da ke jibge a karkashin kasar arewa, wanna zai tabbatar da tattalin arziki ya dawo arewa, shugaba Buhari zai bar tarihi a matsayin shugaban dake da kishin yankin sa.
Shugaba Buhari ya bude kan iyakokin kasar guda 4 bayan da ya kulle su shekara daya da ta wuce, shima ci gaba ne amma shugaba yayi hakuri a shigo da kayan abinci masamman shinkafa domin a bari kasuwa ta tantance tsakanin ta gida da ta waje wajen yin gogayya da farashi da inganci.

Daga karshe, muna taya shugaba Buhari tare da iyalinsa murnar cika shekaru 78 a raye, muna fata Allah ya karo masa shekaru masu albarka cikin imani da tausayi da karbar shawarwarin da zasu kawowa yankin arewa da kasa bakidaya alkhairi da ci gaba.
